Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kuɗi

1
547

A ranar Laraba ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi na Naira 200, N500 da kuma N1,000 a zauren majalisar da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.

An ƙaddamar da sabbin takardun ne gabanin taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako-mako (FEC), wanda shugaba Buhari ya jagoranta.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, a bisa tsarin da ake yi a duniya, ya kamata a sake fasalin kudin Naira, sannan a sake fitar da shi tsakanin shekaru biyar zuwa takwas.

Gwmanan bankin ya yi nadamar cewa a Najeriya kimanin shekaru 19 kenan ba a sake fasalin Naira ba saboda rashin kishi daga shugabannin da suka gabata.

“A baya, dole ne in furta cewa an ci karo da yunkurin CBN na sake fasalin da sake fitar da takardar kudin Naira.

“Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne kadai ke da ƙarfin gwiwar yin hakan,” in ji Emefiele.

Emefiele ya ƙara da cewa, hukumar CBN ce ta sake yin kwaskwarima da sake fitar da takardun, inda ya tabbatar da cewa daga yanzu za a gudanar da tsarin sauya kuɗin duk bayan shekaru biyar zuwa takwas.

“Bayan yau, CBN zata fara sake fasalin da kuma sake fitar da Naira duk bayan shekaru biyar zuwa takwas,” inji shi.

Gwamnan na CBN ya ce jami’an tsaro za su sanya ido kan mutanen da ke cire kudi a kan titin domin sanin nawa aka ciro tare da sanya ido kan yadda ake amfani da kuɗaɗen.

Ya ce babu buƙatar a riƙa cewa manufar ta shafi kowa ne.

Emefiele ya ƙara sa cewa , CBN ta ƙuduri aniyar ganin an bi tanadin dokar adadin kuɗin da mutum ya kamata ya ɗauka.

“Duniya ta koma tsarin amfani da kuɗi batare da takardu ba, (cashless), kuma CBN itama tabi wannan chanji.

” Za mu yanke adadin kuɗin da wani zai cire a rana, za mu bi diddigin bayanan mutumin don sanin dalilin cire wannan kuɗin.

Ga masu kira da a ƙara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗi, shugaban na CBN ya ce, “ba za mu tsaya munabin ra’ayin mutanen da ke son ƙarin lokaci ba.

“Daga yau da aka fitar dqwannan doka zata fara ƙirga kwanakin.”

Ya ce babu ƙaramar hukuma a ƙasar da babu wakilin banki, inda ya ce akwai guri sama da miliyan ɗaya a faɗin ƙasar nan da ya kamata mutane su je su ajiye tsofaffin takardun kuɗinsu.

Emefiele ya kuma ba da tabbacin cewa sabbin takardun ba za a iya yin jabu ba saboda abubuwan da ke cikin su.

1 COMMENT

Leave a Reply