Shirin taimakon ilimin karkara a Najeriya ya lashe kyautar ‘Confucius UNESCO’

0
113
Shirin taimakon ilimin karkara a Najeriya ya lashe kyautar ‘Confucius UNESCO’

Shirin taimakon ilimin karkara a Najeriya ya lashe kyautar ‘Confucius UNESCO’

Lamarin ya samo asali ne a Najeriya, inda rikice-rikice ya haifar da ƙaruwar yawan yara da suka yi Hijira, shirin ‘FastTrack’ na shirin taimakon ilimin Karkara an tsara shi ne don cike giɓin da ke tattare da koyan harshe da haɓaka ƙwarewar yara a sansanonin ‘yan Gudun Hijira da kuma mutanen da ke gudun Hijira (IDP).

Sanin muhimmancin buƙatu a Arewa maso Gabashin Najeriya, inda matsalar ilimi ta shafi yara sama da miliyan 5, shirin ‘FastTrack’ na wayar da kai yana ba da tallafi mai mahimmanci don tabbatar da cewa yaran sun sami ilimin da suke buqata.

‘FastTrack’ ya ƙoƙarin haɗa tsarin ilimin harsuna da yawa wanda ba wai kawai ya tsaya kan inganta ilimin karatu bane, a a har ma da inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban.

Shirin ya ɗauki salon tsarin koyar da harsuna biyu, yana koyar da harshen kasa da kuma asalin harshen da ɗalibi ke magana da shi na asalii.

Wannan hanya ta tabbatar da inganci wajen inganta hadin gwiwar al’umma, samar da zaman lafiya da kuma taimaka wa dalibai su fahimci bambancin al’adu, rage son zuciya, da karin tausayawa.

Hanyar ‘FastTrack’ game da ilimi tana da karfi gami da ɗaukar hankali, musamman an giuna ta ne don magance ƙalubale daban-daban da yaran da da ba su da muhalli ke fuskanta kowace rana.

KU KUMA KARANTA: Za a yi babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya don iganta ci gaba

A cikin mahalli masu rauni da hargitsi, wannan daidaitawar tana da muhimmanci.

Domin magance rikice-rikice na ilimin harsuna da yawa, ‘FastTrack’ na ba da damar samun fasaha mai mahimmanci tare da mai da hankali kan tallafi na mutane daba-daban.

Wannan cakuduwar dabarun suna magance batutuwan da suka zama ruwan dare, kamar ƙarancin malamai masu fahimtar yare biyu, waɗanda za su iya kawo cikas ga tsarin ilmantarwa a wurare daban-daban na harshe.

Bugu da ƙari, shirin yana yin bayani kan haɗaɗɗen aiki na fassara daidaituwar abin da ilimi ya kunsa zuwa yaruka da yawa, don tabbatar da cewa duk abubuwan da ake nufi sun dace da al’ada da mahallin.

Ma’aunin tasirin ‘FastTrack’ shi ne, hanyar nagartacciyar kima, gami da girman zamantakewa da tunani.

Wannan tantancewar na auna nasarar shirin wajen cusa sanin asali da zama dan kasa a tsakanin ɗalibai, ta yadda zai ba da gudummawa ga zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Haɗin gwiwar al’umma shi ne mabuɗin hanyar ‘FastTrack’s’. Sabbin kayan aikin kamar littafin Mavis Talking da alqalami, hade da ingantattun hanyoyin koyarwa, tabbatar da cewa ilimin harsuna da yawa yana samun dama kuma mai jan hankali.

Waɗannan kayan aikin suna sauƙaƙe koyo cikin harshen uwa na dalibi, wanda daga nan ya hadu zuwa ilimin Turanci, yana mai da tsarin ilimin ya zama mara illa kuma. Yunkurin ‘FastTrack’ na gina zaman lafiya yana bayyana a cikin ayyukansa na ilimi wadanda ke haɓaka rashin tashin hankali da mutunta juna.

Shirye-shiryen da aka hada da shirin sun wuce karatu da ƙididdigewa, suna haɓaka amintattun wurare masu kyau wadanda ke kare yara daga tashin hankali da taimako a qoqarin samar da zaman lafiya.

A hangen nesansa, ‘FastTrack’ na da burin fadada shigarsa fadin Afirka, musamman a Sansanonin ‘Yan Gudun hijira a Nijar, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Uganda, da Ruwanda.

Manufar ita ce a kafa wata al’umma mai aiki da za ta aiwatar da hanyoyin ‘FastTrack’ a cikin sassa daban-daban, domin tabbatar da cewa an ga fa’idodin shirin masu zurfi.

A Ranar Rubuce-rubuce ta Duniya, ‘FastTrack’ yana aika sako mai karfafawa ga duk wanda ke da hannu a cikin shirye-shiryen karatu: rungumar mahallin, daidaito, da shaida a samar da ilimi mai mahimmanci.

Za mu iya inganta sakamakon karatu da kuma inganta hadaddiyar jama’a, zaman lafiya ta hanyar daidaita ayyukan ilimi tare da al’adu na ɗalibai.

Amincewa da ‘FastTrack’ ta hanyar 2024 ‘UNESCO Prize Confucius Prize for Literacy’ yana nuna mahimmancin duniya game da manufarsa da kuma yiwuwar sanya ƙwarin gwiwar irin wannan himma a duk duniya.

Leave a Reply