Rikicin Filaye: ABU Ta Mayar Da Martani Ga KDSG, Ta Musanta Siyar Da Filin Ta

0
326

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A SAKAMAKON jin wata sanarwa wacce babban Daraktan Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA) Malam Isma’il Dikko ya yi bisa zargi cibiyar da sayar da filin ta, ya tayar da hankulan hukumar Jami’ar Ahmadu Bello inda ta musanta zancen sayar da filin mai kusan hekta 80 zuwa Kwalejin Aikin Gona da Dabbobi da ke Mando a cikin garin Kaduna ga daidaikun mutane.

A cikin wata sanarwa da aka sanya wa hannu Daraktan Hulda da Jama’a,
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Malam Auwalu Umar ya ce zargin karya ne kuma ba shi da tushe, don Jami’ar Ahmadu Bello ba ta taba sayar da fili ga kowa ba, walau mutum ko kungiya, kuma ba za ta taba yin haka ba.

Ya ce “Kwalejin na da takardar shaidar mallakar (G.ITEM-No.1060) na daukacin kasar da aka kafa ta, baya ga Tsarin Binciken da ke nuna dukkan iyakokin Kwalejin”.

Auwalu Umar ya kara da bayyana cewa hukumomin Jami’ar sun yi wa kwalejin katanga ne shekaru da dama da suka gabata domin hana masu satar filayen su shiga kasarta. Sai dai a kwanakin baya KASUPDA da ake zargin tana aiki da umarnin gwamnatin jihar Kaduna, ta keta ka’ida ba bisa ka’ida ba, sannan ta rusa katangar da ke kan iyakokinta cikin rikon sakainar kashi, duk kuwa da umarnin kotu na ci gaba da dakatar da hukumar daga irin wannan haramcin.

“Hakika Darakta Janar na Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA), Isma’il Dikko, ya yi karya ta hanyar zargin hukumar da sayar da filayen ta ga daidaikun mutane.

Ya koka da yadda KASUPDA ta gaza yin gwaji mai sauki na gudanar da sahihin bincike don kaucewa kunyatar da gwamnatin jihar, watakila saboda tsananin son zuciya da kishinsa ta hanyar yin wannan zarge-zargen da ya yi”.

“Wannan wani mataki ne na ceto fuskar da Isma’il Dikko ya yi amfani da ita bayan da ya gane illar abin da ya aikata da laifin da ya aikata a Jami’ar”.

“Domin kaucewa shakku, ya kamata hukumar kula da tsare-tsare da raya birane ta jihar Kaduna ta san cewa, babu wani abin da zai sa ABU ta bari a karbe filayenta ba bisa ka’ida ba domin rabawa abokan tarayya da sauran marasa kishin kasa”.

Leave a Reply