Remi Tinubu ta ba da naira miliyan ɗari biyar ga ‘yan gudun hijira a Filato

1
382

Damuwa da tashe-tashen hankula a jihar Filato, a ranar Talata, uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta bayar da gudummawar naira miliyan 500 ga iyalai 500.

Waɗanda suka ci gajiyar tallafin dai sun fito ne daga ƙananan hukumomi shida na jihar ta Arewa ta tsakiya.

Sanata Tinubu ta je Jos babban birnin jihar ne domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da ƙarfafa musu gwiwa da ka da su karaya, yayin da maigidanta da sauran masu ruwa da tsaki ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a cikin al’ummomin da ke fama da rikici.

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana damuwarta kan rikicin da ya dabaibaye jihar musamman al’ummar Mangu, inda ta bayyana damuwarta da yadda ta samu labarin ɓarnar rayuka da dukiyoyi.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta mayar wa wata mata miliyan 19 da gida da mota

Uwargidan shugaban ƙasar ta lura da cewa wannan matakin shi ne hanyarta na tallafawa iyalan waɗanda abin ya shafa da matsuguni da sauran muhimman buƙatu.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Caleb Mutfwang, ya yabawa matakin na uwargidan shugaban ƙasar.

Yayin da yake bayyana ta a matsayin shugaba mai tausayi mai kishin bil’adama, Gwamna Mutfwang ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da ka da su kasance masu son kai wajen rabon kuɗaɗen ga ‘yan gidansu.

1 COMMENT

Leave a Reply