NNPP ta shigar da ƙara gaban Kotun Ƙoli kan shari’ar gwamnan Kano

Jam’iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta shigar da ƙara gaban Kotun Ƙolin ƙasar inda take ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya soke nasarar gwamna ɗaya tilo da jam’iyyar ta samu a zaɓen watan Maris.

NNPP ta shigar da ƙarar ce inda ta kafa manyan hujjoji guda goma, tana neman kotun ƙoli ta sake nazari kan hukuncin ƙaramar kotun sannan ta warware ɓangarorin da suka bai wa Abba Kabir Yusuf rashin nasara.

Haka zalika, ta nemi kotun ta tabbatar da ɓangarorin hukuncin da suka bai wa ɗan takararta, gwamnan Kano mai ci nasara.

KU KUMA KARANTA: NNPP ta shirya ƙawance da jam’iyyun adawa

Daga cikin ɓangarorin hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da take ƙalubalanta kamar yadda wata takardar kotu ta nuna, NNPP ta yi iƙirarin cewa sashe na 177 ƙaramin sashe na c, bai fitar da ƙa’ida a kan kasancewar mutum ɗan jam’iyya ba.

Sannan ta ce wani mutum daban ba shi da ikon tuhumar ɗan takarar da ya tsaya takara kuma ya ci zaɓe a inuwar wata jam’iyya, kasancewarsa ɗan jam’iyyar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *