Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
A BISA shirye-shiryen da ta ke na ganin cewa an samu nasarar gudanar da taron ranar ma’aikata na bana tamkar yadda aka saba a duk ranar 1 ga watan Mayu, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), reshen Jihar Kaduna ta fara haramar shirye-shiryen ganin an gudanar da bukin lami lafiya ta hanyar yin tsare-tsare na musamman a Jihar.
Taron na banan mai taken “Matakan Kungiyar Kwadago domin samar da yanayin Shugabanci Nagari da kuma ci gaban Najeriya wanda ya gudana a garin Kaduna a dakin taro na gidan Kungiyar Malamai dake Kabala Kaduna, an shirya shi ne da zummar karawa juna sani ta hanya gabatar da kasidu.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban taron wanda yake sakataren Kungiyar Dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba Ahmad, ya bayyana cewa Ya’yan kungiyar ta (NLC) na da rawar da za su taka ta hanyar shiga cikin al’amuran siyasar kasar dumu-dumu domin a dama dasu a kowani mataki na mulkin kasar.
Ya kara da cewa, a kullum al’amura a kasar na kara tabarbarewa musamman a fannin tsaro da shugabanci, sannan kokarin da Gwamnati ta ke yi ta fannin ganin cewa an samar da duk wasu shugabanci nagari a duk wasu matakai a fadin Kasar hakarsu bata cimma ruwa saboda bata-gurbin da ke cikinsu.
Ya ce “abubuwan da ke faruwa a kasar nan ya yi yawa, ga matsalar rashin tsaro, ga tsananin rayuwa da halin kunci da mutane ke ciki, sannan duk Shugabannin da muka zaba kamar sun juya mana baya, Allah kadai ne bai juya mana baya ba don haka muna rokon Allah da ya kawo mana saukin wannan rayuwa.”
“Ga zabe na tunkaro mu a shekara mai zuwa, ya zama wajibinmu ne mu zabi Shugabanni Nagari kuma tun yanzu ya kamaci musan irin mutanen da zasu wakilce mu a matsayin Shugaban kasa, Gwamnoni da sauran matakai, domin idan da akwai abubuwan da ya kamata mu sake dubawa su zama mana darasi a rayuwa, yanayin shugabancin mu ne.”
“Wannan zaben da za ayi, idan mutanen mu basu zabi mutane masu tsoron Allah ba, toh zamu ci gaba da kasancewa a cikin da muke ciki, sannan mutanen da aka yi garkuwa da yan Uwansu, ya kamata Shugaban Kasa ya neme su a zauna dasu domin nuna tausayi a gare su ta hanyar bayani mai dadi amma a kyalesu haka ba ayi musu adalci face sai wanda yace ba zaizo ba idan aka kira su, sai a kyale shi.”
“Sannan makasudin taruwarmu a nan wanda yake shi ne matsalar Malaman Makaranta ya kamata a sake duba shi domin ko malaman Makarantar da ke Koyar da yara a Makarantar Gwamnati basa kai ‘ya’yansu makarantun sai na kudi wanda hakan ke nuna cewa ba abun kirki suke Koyar da yaranmu ba, don haka muddun ba a gyara ba, yaran da aka hana Ilimi da gata su ne zasu dawo su addabi yaranmu da al’umma.”
Hakazalika, da a nata jawabin, shugabar ma’aikata ta Jihar Kaduna Hajiya Bara’atu wacce ta samu wakilcin Kwamared Shehu Muhammad, ta bayyana cewa Gwamnatin Jihar karkashin Ofishin Shugaban ma’aikatan ta ware wasu makuden Kudade don ganin an samu inganta sashen ma’aikatan ta hanyar basu horon da ya dace.
Ta ce “wannan taron karawa juna sani da wayar da kan al’umma da Kungiyar ta shirya na daya daga cikin irin Matakan da Gwamnatin Jihar ke shiryawa domin tabbatar da an ilimantar da ma’aikatan Jihar ta kowani fanni da suka hada da sashen Ilimi, lafiya da sauran bangarorin ma’aikatun Jihar.
A nata jawabin, Sakatariyar kungiyar ta (NLC), reshen Jihar Kaduna, Kwamared Christiana John Bawa ta bayyana cewa wannan taron da suka shirya na daya daga cikin tsare-tsaren da suke na ganin cewa an gudanar da taron bikin ranar ma’aikatan na wannan shekarar ta 2022 domin kara wayar da kan ma’aikatamsu.
Acewarta, al’amura da dama sun dagule a kasar wanda hakan yasa Kungiyar ta daura damarar ganin cewa ta sanya mutanen ta a cikin Gwamnati domin damawa da su musamman ganin irin yadda wasu Shugabannin da aka zaba ke kyarar ma’aikatan, amma kasancewar mutanen su a cikin Gwamnatin dole zai sanya a rika sauya wasu abubuwan.
Ta ce “har yanzu Gwamnonin wasu Jihar basu tabbatar da kason mafi karamcin albashi ba, kuma wasu basu biya albashin ma’aikatansu na watanni ba sannan a irin haka suke kokarin fitowa takarar neman shugabancin kasar nan don haka muke kokarin ganin kara wayar kan mutanenmu su shiga cikin al’amuran siyasar kasar domin a dama da su saboda samun sauyi.”
A karshe, Sakatariyar Christiana John Bawa, ta shawarci ma’aikata a kowani mataki da su bude idanuwansu kana su rungumi matakan tsunduma cikin harkokin siyasar dumu-dumu ko da ba za su tsaya takara ba.