Nijar ‘yan’uwanmu ne, kar a tura sojoji su yaƙe su – El-Zakzaky ga Tinubu

1
425

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya (Islamic Movement), Shaikh Ibraheem El-Zakzaky ya gargaɗi shugaba Bola Tinubu akan tura dakarun soji a jamhuriyar Nijar, inda ya bayyana cewa suna da tarihi tare don haka ‘yan uwan juna ne.

El-Zakzaky ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga gungun masu karatun Alkur’ani a lokacin da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja.

Shaikh Zakzaky ya ƙara da zargin Faransa da Amurka da son amfani da Najeriya wajen kai wa Jamhuriyar Nijar hari.

“Ba zato ba tsammani, Faransa da Amurka suna son amfani da Najeriya wajen kai wa Nijar hari.

Wannan abin mamaki ne matuƙa ganin yadda Najeriya da Nijar mutane ɗaya ne.

Ko kudancin Najeriya ba haka yake ba, mu a arewacin Najeriya muna da dauloli waɗanda Shehu Usman Danfodio da Kanem Borno suka kafa.

Yankunan irin waɗannan masarautu ne aka yayyanka don samar da Nijar da Najeriya.”

KU KUMA KARANTA: Ecowas za ta gudanar da taron ƙoli kan Nijar a Abuja

“Na taɓa gaya muku Gazargamu babban birnin Kanem Borno ne ko? Katangar birnin ba ta cika ba saboda har yanzu akwai ragowar gine-ginen.

Yana iya ba ku sha’awa ku lura cewa rabin katangar tana gefen iyakar Nijar ne, sauran kuma tana cikin Najeriya. Lokacin da aka raba kan iyakokinmu, ba su ɗauki tarihinmu a cikin sani ba.

“Kamar yadda nake gaya muku, an raba yankin Borno gida huɗu, Najeriya, Kamaru, Chadi, da Nijar.

Yawancin yankin na Borno ne. Bugu da ƙari, idan aka duba yankin daular Shehu Usman, daga Borno har zuwa Sakkwato, an raba kowane gari gida biyu”, inji shi.

El-Zakzaky ya ci gaba da cewa, “Idan ka duba yankin Haɗeja, an mayar da wani yanki nasa zuwa Nijar. Wani yanki na yankin Gumel wani yanki ne na Nijar.

Idan ka haye kan iyakar Maigatari, har yanzu kana cikin yankin Gumel amma an miƙa wani yankin ga Nijar. Wani sashe na Kazaure ma yana cikin Nijar ne.”

“Wannan ita ce makomar Daura. Wani babban yanki na Daura shi ma ya zama yankin Nijar.

An kuma raba Katsina gida biyu: Katsinan Maraɗi da Katsina ta Najeriya. An raba su duka. Haka kuma an raba daular Gobir tsakanin Nijar da Najeriya. Garin da aka haifi Shehu Usman Ɗanfodio, Marata, yana cikin Nijar.”

Ya ce alaƙar al’adu da Nijar da Najeriya ke da su ya fi kusanci fiye da yadda mutane ke zato, inda ya bayyana cewa su tagwaye ne, tushensu da ɗabi’u ɗaya ne. “Su ’yan’uwanmu ne, tun da yake garin mahaifinmu Shehu Ɗanfodiyo, yana cikin ƙasarsu.

Abin mamaki ne yadda waɗannan marasa tausayi suke so su yi amfani da ƙasar nan su kai wa ’yan’uwanmu hari, don kawai su yi kisan kiyashi na ’yan’uwa, ko?” “Na ji cewa wasu ‘yan Nijar sun yi iƙirarin cewa Najeriya za ta kai musu hari. Ina ba da shawarar ku daina wannan tunanin.

Ko da barazanar mamayewa ta bayyana da gaske, Allah Ya kiyaye, ba mu ne muke kawo muku hari ba. Hannun wani mai iko ne a bayan fage tare da haɗin gwiwar shugaban ƙasa za su kawo muku hari, amma ba ’yan Najeriya ba.

“Ba a tuntuɓe mu ba, ba ma goyon bayansa, kuma babu yadda za a yi mu kashe juna.

Don haka ba Najeriya ce za ta kai hari ba, wasu ƙasashen waje ne ke son yin amfani da Najeriya wajen yin hakan. Sun saba da wannan.

“Sun taɓa yin hakan bayan juyin juya halin Musulunci a Iran lokacin da suka yi amfani da Saddam Hussein wajen mamaye Iran.

Yaƙin dai ya shafe shekaru 8 ana gwabzawa yayin da mutanen Iran da Iraƙi al’umma ɗaya ne. Dangantakar al’adu da suke da ƙarfi ta yadda wani ɗan Iraƙin ke riƙe da wani babban muƙami a Iran.

“Ayatullah Sahrudi wanda shi ne babban alƙalin kasar Iran, dan ƙasar Iraƙi ne. Shi ne babban alƙalin ƙasar Iran.

Za ku ga makamai da yawa da ‘yan Iraƙin ke ba su, kuma babu wanda ya tayar da gira a kan lamarin kawai saboda suna ganin juna ɗaya.”

1 COMMENT

Leave a Reply