Nicolas Maduro, Shugaban ƙasar Venezuela ya sake lashe zaɓe

0
47
Nicolas Maduro, Shugaban ƙasar Venezuela ya sake lashe zaɓe

Nicolas Maduro, Shugaban ƙasar Venezuela ya sake lashe zaɓe

Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a ranar Lahadi, in ji Hukumar Zaɓe ta ƙasar.

A sanarwar da ya fitar, shugaban hukumar zaɓen Elvis Amoroso ya ce an ƙirga kashi 80 na ƙuri’un da aka kaɗa kuma Maduro na jam’iyyar GPP ne ya yi nasarar lashe kujerar shugaban ƙasa a tsakanin ‘yan takara 10.

Sakamakon farko na zaɓen ya ayyana Maduro ya lashe kashi 51.2 inda zai yi wa’adi na uku a kan mulki.

Ɗan takarar ƙawancen ‘yan adawa na UDP Edmundo Gonzalez Urrutia ya zo na biyu da kashi 44.2.

Sai dai kuma, ƙawancen ‘yan adawar a ranar Litinin ɗin nan ya yi watsi da nasarar da aka ce Maduro ya samu, yana mai cewar sun samu kashi 70 na ƙuri’un, ba wai kashi 44 da hukumar zaɓe ta bayyana ba.

KU KUMA KARANTA: Shugaban Rwanda, Kagame, ya lashe 99% na ƙuri’un da aka ƙirga a zaɓen shugaban ƙasa

“Muna son shaida wa dukkan ‘yan Venezuela da duniya baki ɗaya cewar Venezuela na da sabon shugaban ƙasa da aka zaɓa wato Edmundo Gonzelaz Urruta,” in ji wata shugabar ‘yan adawa Maria Corina Machado yayin tattauna wa da ‘yan jarida. Ta ƙara da cewa “Mun yi nasara”.

Amoroso ya ƙara da cewa za a buga cikakken sakamakon zaɓen a shafin intanet na hukumar a awanni masu zuwa. An lura cewa an samu fitar masu jefa ƙuri’a da kashi 59.

A ranar 10 ga Janairu, 2025 za a rantsar da mutumin da ya yi nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here