Neman Adalci a Kotunan Najeriya: Zakaran gwajin dafi ne ga haƙurin jama’a

0
69
Neman Adalci a Kotunan Najeriya: Zakaran gwajin dafi ne ga haƙurin jama'a

Neman Adalci a Kotunan Najeriya: Zakaran gwajin dafi ne ga haƙurin jama’a

Daga Yusuf Alhaji Lawan

Neman adalci ginshiƙi ne na ‘yancin ɗan Adam, da ke ƙumshe a kundin tsarin mulki na kowace ƙasa da ke tafiya akan tsarin dimokuraɗiyya. Sai dai a Najeriya wannan ‘yanci ya zama kamar wata alfarma da kaɗan ne ke iya samu.

Ɓangaren shari’a na Najeriya, an tsara shi ne domin tabbatar da adalci da kare ‘yancin ‘yan ƙasa, amma kuma ya zama abu na jinkiri da yake haifar da takaici da damuwa.

Ga ‘yan Najeriya da dama, neman adalci wani abu ne mai nauyin gaske da ke buƙatar tsananin haƙuri da juriya da kuma sa’a. Tsarin yana gajiyarwa kuma hakan na sa wasu su yanke ƙauna.

A matsayi na na wanda ba shi da alaƙa da abin da ya shafi harkar shari’a, mai ƙoƙarin kiyaye dokoki domin na zauna lafiya, ina da ƙarancin hulɗa da harkokin kotu. Duk da haka, tattaunawa da abokai da sauran jama’a da kuma bibiyar abubuwan da ke kai kawo na al’amurran yau da kullum, sun sa ina takaicin labaran da ke yawo akan ɓangaren shari’a na ƙasa.

A kwanaki baya, na samu alaƙa da harkar kotu saboda wani da na sani da ya gamu da tsautsayin hatsarin mota. Saboda kusanci na da muhallin da abin ya faru, na shiga cikin maganar domin na ba da gudunmowa, musamman da ya zama shi mai motar yana nesa sosai.

Hatsari ne da ya shafi mota biyu, babba da ƙarama, amma cikin taimakon Ubangiji, babu wanda ya samu rauni, don hatsarin ya taƙaita akan motocin.

Amma duka motocin biyu an ajiye su a ofishin ‘yan sanda mafi kusa da wurin da abin ya faru, wanda yanzu haka sun kusan shekara guda kenan ana jiran umarnin kotu.

A yayin gudanar da shari’ar, sai ɗaya daga waɗanda abin ya shafa ya bayyana rashin gamsuwa akan yadda alkali ke gudanar da al’amarin shari’ar, sai ya ɗaukaka ƙara zuwa kotu ta gaba da buƙatar ayi bita akan yadda alkalin farko ke gudanar da shari’ar da kuma soke umarninsa na farko daya gabatar.

Bayan lauyoyi sun yi musayar ra’ayoyi a rubuce kuma an zauna a babbar kotu an tattauna, kotu ta ayyana rana ta yanke hukunci, wacce an ɗaga wannan rana kusan sau huɗu. A yanzu haka, babu wanda zai iya bugar ƙirji ya ce ga yadda sakamako zai kasance, amma yana iya zama ɗayan biyu.

KU KUMA KARANTA: Amfani Da Hoton Wani A Shafinka Na Sada Zumunta: Dacewa ko akasin haka?, daga Yusuf Alhaji Lawan

Ko dai ita babbar kotu ta bayyana gamsuwa da yadda alkalin farko yake gudanar da shari’ar, tace a koma yaci gaba, ko kuma ta bayyana rashin gamsuwa, don haka ta ayyana wani alkali na wata ƙaramar kotu ya karɓi shari’ar. Idan na biyun nan ya kasance, to za’a sake fara shari’ar kenan daga farko, kuma kusan shekara guda da aka yi ta zama a banza.

Saboda rashin jin daɗi kan yadda harkokin wannan shari’ar ke tafiya ne yasa na samu wani abokin aiki na, wanda shi lauya ne, na ba shi labarin halin da ake ciki, cikin murmushi yace mini ai ɓata shekara guda akan shari’a a Najeriya ba komai ba ne, abu ne da aka saba. Kun yi sa’a ma mota aka tsare ba mutum ba.

Yace a kotun ɗaukaka ƙara, suna iya daga zaman shari’a suce a dawo bayan shekara biyu, kotun koli kuwa tana iya dage zaman shari’a zuwa shekara biyar. Kalaman sa sun girgiza ni sosai.

Abin da na fahimta dangane da wannan shari’ar da kuma wasu guda biyu da na saka ido akai a wasu wurare, lallai sun saka na canza kallo da nake yi wa ɓangaren shari’a.

Nauyin da ya ke kan alkalai na da girma sosai wanda ko a wane irin yanayi na walwala na gansu ba zan yi ƙyashin su ba, domin sauka gaban Allah a irin wannan yanayi akwai tashin hankali babba. Dawainiya ce da ban yi wa wani fata ba.

Idan da zan ba da shawara, sai ince duk yanda mutum zai yi, to ya kiyaye duk wani abu da zai kai shi yin shari’a a kotun Najeriya. Takaici da ɓacin rai na da yawa a ciki sosai.

Na fahimci cewa muhimman ayyukan alkalai na gudanar da shari’a a kotuna na samun tasgaro saboda wasu ayyuka na daban da suke shiga da suka shafi ayyukan komiti, zuwa ayyukan kwanan-daji da kuma yawan zuwa hutu.

Waɗannan na daga abubuwan da ke kawo tsaiko da jinkiri wajen gabatar da shari’o’i akan lokaci. Wannan kallo ne daga nesa, mai yiwuwa da za’a matsa kusa, haƙiƙa ɗin da za’a gano za ta iya wuce haka.

A nan za’a iya cewa fata da ‘yan ƙasa suke da shi akan mulkin dimokuraɗiyya ba’a cimmasa ba. Jinkiri wajen samar da adalci ba shi ne tsammanin jama’a ba.

Samuwar matsaloli a ɓangaren shari’a wajen jinkiri ko rashin samar da adalci ga masu ƙorafi da waɗanda aka zalunta na da nasu gudunmowa wajen kawo cikas a aikin gina ƙasa da bayyana gazawar dimokuraɗiyya da bin dokoki. Rashin ɗabbaƙa adalci ko samun sa da jinkiri na saka ‘yan ƙasa su ba da gari akan tsare-tsaren gwamnati.

Masu sanya jari kuma gwuiwar su za ta iya yin sanyi wajen sanya kuɗin su a cikin ƙasar da tsarin shari’ar ta ba zai ba da tabbacin kariya ga rayuka da dukiyoyin su ba.

Sannan tsarin shari’a da ya ke da rauni zai iya ba da ƙofa ga rashawa, ƙin bin doka, yamutsi da rashin tabbas. Wannan kuma zai iya hana ci gaban ƙasa kuma ya raunana gwamnati a idon jama’a musamman na rashin cika alƙawuran ta da kuma yin barazana ga ƙasa.

Jinkiri wajen tabbatar da adalci na yin tuni ga ƙalubale da ke bibiyar ɓangaren shari’a a Najeriya. Idan na tuna maganar abokin aiki na, sai na ƙara tabbatar da cewa bibiyar harkokin shari’a a kotunan ƙasar nan, lallai zakaran gwajin dafi ne ga haƙurin mutane saboda jinkiri da sarƙaƙiya da ke cikin harkokin shari’a.

Tare da cewa jiran adalci na gajiyarwa, amma kuma ya na da muhimmanci sosai a ci gaba da fadi-tashi na ganin an aiwatar da sauye-sauyen da za su ƙarfafa ɓangaren shari’a waɗanda za su tabbatar da samun dama zuwa ga adalci akan lokaci.

Yusuf Alhaji Lawan ya rubuta daga Anguwar Hausawa Asibiti, Garin Potiskum, Jihar Yobe. Za’a iya tuntubar sa ta nasidi30@gmail.com.

Leave a Reply