NAHCON ta sanar da yadda Saudiyya ta rage kuɗin aikin Hajjin bana

0
230

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun yi ragin kuɗin Hajji ga maniyyatan da za su sauƙe farali a bana, 2024, domin farantawa mahajjata.

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar cewa shugabata, Jalal Ahmad Arabi, ne ya nemo ragin da aka yi, wanda ya shafin kuɗin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake wa alhazai a Saudiyya.

Mai magana da yawun hukumar NACHON, Fatima Sanda Usara ce ta sanar da hakan a ranar Laraba, inda ta ce a sakamakon haka, Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kuɗin tikitin jirgin da aka biya a 2023, masauki a Madina daga Riyal daga 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu

“Zama a Muna da Arafa da Muzdalifa kuma an rage shi zuwa Riyal 5,393 zuwa 4,770,” in ji ta.

Sai dai duk da haka, sanarwar ba ta bayyana ko NAHCON za ta yi wa maniyyayatan Najeriya ragin kuɗin kujera daga naira miliyan 4.5 da ta sanar tun da farko ba.

Kazalika ana hasashen duk da sauƙin da wannan Saudiyya ta yi, da wuya maniyyayatan Najeriya su shaida sauƙin — daga naira miliyan 3 da suka biya a 2023 — sakamakon tashin farashin Dala.

Farashin kuɗaɗen ƙasashen waje musamman Dala sai ƙara ƙaruwa yake a Najeriya, lamarin da ke ƙara haifar da tsadar rayuwa a ƙasar.

Akasari ana biyan kuɗin aikin Hajji da sauran huldodin ƙasa da ƙasa, kamar aikin Hajji da sauransu ne da Dala ko sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.

Faɗuwar darajar kuɗin Najeriya, naira da tashin dala da danginsa a ƙasar ta sa a duk shekara kuɗin aikin Hajji ƙaruwa.

A sakamakon haka ne aka samu ƙarin kashi 50 a kuɗin aikin Hajjin 2024 a kan na 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu raguwar maniyyayatan Najeriya da za su sauƙe farali a bana a sakamakon tsadar kuɗin kujera.

Leave a Reply