NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce ƙasar Saudiyya ta ba maniyyatan ƙasar nan da mako uku su fara biyan kafin alƙalami na kuɗaɗen kujerar aikin hajjin shekara ta 2024.

A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, ta ce Saudiyya ta ajiye ranar 4 ga watan Nuwamba domin kammala shirye-shiryen da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar.

Ta ce bayan nan ne hukumar za ta tantance ainihin yawan maniyyatan wanda daga nan ne za ta tattauna batun farashin kujera, har kuma ta yanke shi daga ƙarshe.

Fatima ta kuma ce shirye-shiryen da hukumar ta fara yi ne suka sa a yayin tattaunawar shugabannin Hukumomin Alhazai na jihohin Najeriya a kwanakin baya ta sanar da Naira miliyan huɗu da rabi a matsayin kuɗin kujera a hajjin baɗi.

KU KUMA KARANTA: An bayyana kuɗin da maniyyata aikin hajjin 2024 za su ajiye a Kano

Sanarwar ta ce, “Da farko dai dalilai uku ne suka sa za a fara ajiye waɗannan kuɗaɗen na kafin alƙalami. Na farko shi ne saboda jihohi su san yawan alhazan da za su biya kuɗin, aƙalla kafin nan da ranar 4 ga watan Nuwamba, wanda shi ne lokacin da Saudiya ta sanya domin kammala shirye-shiryen dukkan masu ruwa da tsaki.

“Yin hakan zai taimaka wa hukumomin yin dukkan tsare-tsaren da suka kamata a kan lokaci.”

Sai dai ta ce an amince daga bisani za a ba maniyyatan dama su cika ragowar kuɗaɗen sannu a hankali zuwa lokacin da za a sanar da ainihin farashin kujerar.

Ta kuma ce duk waɗanda suka gaza biyan adadin da aka fara ƙayyadewa, to su kuka da kansu idan aka ƙirga yawan maniyyatan babu sunansu.

Sai dai ta tsaya kai da fata cewa har zuwa wannan lokacin, akwai yiwuwar mafi ƙarancin farashin kujerar a baɗi ya kai naira miliyan huɗu da rabi, kamar yadda hukumar ta sanar a kwanakin baya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *