MƊD ta bayyana damuwa kan ƙaruwar tashin hankali a Sudan

0
2498
MƊD ta bayyana damuwa kan ƙaruwar tashin hankali a Sudan

MƊD ta bayyana damuwa kan ƙaruwar tashin hankali a Sudan

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana damuwarsa ga hafsan hafsoshin sojin Sudan a game da yadda ricikin kasar yake dada ruruwa, yayin da suka gana a wani taron manyan jakadu a birnin New York a ranar Laraba.

Kafanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, Babban sakateren ya bayyana damuwa matuka a game da ta’azarar rikicin na Sudan, wanda yake ci gaba daidaita rayuwar fararen hula ‘yan Sudan sannan yake tattare da hadarin yiwuwar bazuwa a yankin” Kamar yadda wata sanarwar ganawar da Guterres ya yi da Abdel-Fatah Al-Burhan ta kunsa.

A wani ɓangaren kuma, Amurka za ta bai wa al’ummar Sudan ƙarin kuɗin tallafin agajin jin-kai na dala $424, abin da jakadar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Linda Thomas Greenfield ta sanar a ranar Laraba kenan.

A tsakiyar watan Afirilun bara ne yakin ya barke a sanadiyyar rikicin neman iko tsakanin sojojin sojin kasar ta Sudan SAF da kuma mayakan Rapid Response Support Force gabann shirin mika mulki ga mulkinfararhula a kasar.

KU KUMA KARANTA: Israila tana shirin kai farmaki a wani sansanin yan gudun hijira a Gaza

Sama da ‘yan Sudan miliyan 25 ne suke fuskantar mummunar matsalar yunwa.

Da dama daga cikin su suna fama da rashin abinci (yunwa) sannan wasu miliyan 11 kuma sun gudu daga gidajensu a wani yanayi da ya zama babbar matsalar jin-kai mafi muni a duniya a cewar Ambassada Thomas-Greenfield.

Dubban ‘yan gudun hijirar da rikicin Sudan ya rutsa da su.
“Wajibi ne ɓangarorin biyu da ba sa ga maciji su amince su jinkirta faɗan bisa dalilin buƙatu na jin-kai a al-Fashir, Khartoum da sauran yankunan da suke cikin mumunan yanayin buƙata.

Wakilin Reuters Michelle Nicholas ya ruwaito cewa, Sanarwar ta ce jumullar kuɗaɗen da Amurka ta kashe don ba da tallafin jin-kai tun daga farkon rikicin ya kai dala biliyan$2, a bayanan ofishin Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Leave a Reply