Mun tafka babban kuskure da muka rungumi dimokraɗiyyar turawan yamma – Obasanjo
Daga Idris Umar, Zariya
Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce ƙasashen Afrika ciki har da Najeriya sun tafka babban kuskure da suka rungumi dimokraɗiyyar turawan yamma.
Obasanjo ya bayyana haka ranar Litinin, lokacin da mambobin Majalisar Tarayya masu hanƙoron sake dawo da mulkin irin na tsarin Jamhuriya ta Farko, wato ‘parliamentary’, suka kai masa ziyara a Abuja.
‘Yan Majalisar waɗanda ke ƙiran gungun su “Parliamentary Group” a ƙarƙashin Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda, ɗan PDP daga jihar Ribas, sun gana da Obasanjo a Cibiyar Taro ta Shehu ‘Yar’Adua, a babban birnin tarayya.
Ganawar na daga cikin tsare-tsaren gungun ‘yan majalisar, inda suke bi suna kai wa wasu fitattun ‘yan Najeriya ziyara, domin neman goyon bayan su na ƙoƙarin soke tsarin shugaban ƙasa, a koma tsarin firai-minista.
Obasanjo wanda ya yi mulkin soja daga 1976 – 1979, shi ne ya jagoranci kafa dokar Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1979, wanda ya samar da tsarin shugaban ƙasa mai cikakken iko, irin tsarin dimokraɗiyyar Amurka. Wannan tsari ne kuma ya maye gurbin tsarin firayi minista tun a lokacin a Najeriya.
KU KUMA KARANTA: EU ta sake jaddada aniyar ƙarfafa dimokraɗiyyar Najeriya
A 1999 kuma Obasanjon ne aka zaɓa ya zama shugaban ƙasa mai cikakken iko, shekaru 20 bayan kafa tsarin. Ya shafe shekaru takwas ya na mulki.
Kafa Tsarin Mulkin Dimokraɗiyyar Turawan Yamma Kuskure Ne:
Da yake bayani kan dimokraɗiyya a Afrika, Obasanjo ya ce ƙasashe a wannan nahiya sun tafka kuskure da suka rungumi dimokraɗiyyar Turawan Yamma, wadda ƙirƙirar Turawa ce.
Ya ce dimokraɗiyyar Turawan Yamma ba da tafiya daidai da tsarin ɗabi’un zamantakewar ‘yan Afrika.
“Bari na koma daga farkon inda muka tafka kuskure, shi tsarin mulkin dimokraɗiyya na Turawan Yamma, idan ka kalle shi tsaf, ɓurɓushin ɗabi’un sune a tarihance. Al’adun su ne kuma tsarin rayuwar su ce.
“To na dubi tsarin rayuwa da ɗabi’u da al’adu da yaren ƙasashen Afrika da dama. Shi tsarin dimokraɗiyya ya bayar da ‘yancin yin biyayyar adawa.
To a Afrika kuma menene adawa? Abokin gaba. Dimokraɗiyyar Turawan Yamma na adawa amma su na biyayya ga sarakunan gargajiyar su. Daga nan dimokraɗiyyar kacokan ta fara. Saboda sarakunan gargajiya ne a wancan lokacin ke mulkin su.
“Amma kwata-kwata tsarin mulkin dimokraɗiyya na Turawan Yamma ya raba hanya da al’adu, ɗabi’u da rayuwar zamantakewar ‘yan Afrika.
“Ai dama can tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka muna mulkar kanmu da kanmu. Muna da dauloli a wancan lokacin, muna kuma da manyan masarautu. Ba mu mulki kan mu a matsayin masu adawa ba.
“Ina ganin mu tsarin mulkin mu na lokacin shi ne ‘dimokraɗiyyar Afrika.” Inji Obasanjo.
Ya ce ya amince da ƙoƙarin da waɗannan gungun ‘yan majalisa ke yi, saboda akwai buƙatar sauya salon taku da alƙiblar tsarin mulki a Najeriya da Afrika baki ɗaya.
Sai dai kuma ya yi gargaɗin cewa su guji yin gaggawa. Akwai buƙatar su yi tsari mai dogon zango, kuma su yi taka-tsantsan.
Ya ba su shawara su watsar da batun parliamentary system” da suke ƙiran takensu, su koma “homegrown democracy”, wato dimokraɗiyyar cikin gida.
“Saboda idan ku ka ce sai tsarin firayi minista za a yi, to za ku ci karo da mutanen da su kuma za su ce ba su son tsarin firayi minista.” Inji Obasanjo.
Dalilin Mu Na Ɗaukar Tsarin Firayi Minista – Chinda:
A lokacin da ya ke wa Obasanjo jawabi, Chinda ya ce sun ɗauki tsarin “firayi minista saboda babu wata kalma da suke ganin ta fi hakan dacewa a wannan kamfen da suke yi.
Ya ce su ma tsarin da suke so a bijiro da shi, tsarin cikin gida ne. Ba mai fassara ba tsarin firayi minista ba ne daga littafi kai tsaye.
Masu wannan ƙumaji dai na so a saki tsarin shugaba mai cikakken iko a cikin 2031.
Cikin watannin baya sun gana da Ango Abdullahi, Bisi Akande, Sanusi Ɗantata da sauran su.