Muhimmancin shayar da yaro nonon uwa

0
34
Muhimmancin shayar da yaro nonon uwa

Muhimmancin shayar da yaro nonon uwa

Daga A’isha Kazimiyyah

A bincike Ma’aikatan Lafiya ya nuna cewa nonon uwa yana da gagarumin tasirinsa a kan jarirai, musamman wajen haɓakar lafiyar Jarirai ɗin, wanda ya haɗa jiki da na ruhin Jarirai ɗin.

Sannan ya zo a ruwaya cewa gudanar da karatun alkur’ani tare da ambaton Allah da addu’o’i a lokacin shayar da jariri, yana da fa’ida wajen kare Jarirai.

Kamar yadda nonon uwa ke da tasiri a fagen magance matsalar ɓullar tamowa ta hanyar ƙara lafiyar jikin jariri da samar masa da lafiya da nutsuwa.

Tabbas nonon uwa shi kaɗai zai riƙe jariri har zuwa watanni shida, kuma zai samar masa wasu sinadaran girman jiki da lafiya, don haka a tsawon wannan lokacin babu buƙatar uwa sai ta shayar da shi ko ciyar da shi wani nau’in abinci da ba ruwan nonon ta ba.

Kamar yadda yazo a cikin wata ruwaya, Imam Ja’afar Sadiq (AS) yana wasiya ga matarsa cewa; “Shayar da jariri nono daga dukkanin bakin nono biyu yana wadatar da jariri daga ruwa da abincin da yake buƙata”.

Wato Ma’anar Imam na faɗin haka shi ne, “shayar da jariri daga bakin nono guda yana matsayin ruwan da yake buƙata ne, sannan shayar da shi daga daya bakin nonon yana matsayin abincin da ke buƙata”.

Hakanan idan kuma muka dawo kan Malaman sanin lafiyar Ɗan Adam, za mu ga cewa Likititi sun yi bincike na ilimi, kuma ilimin ya tabbatar da cewa; “Ruwan nonon da ke fara fitowa mai ruwa-ruwa a lokacin da mahaifiya zata shayar da jaririnta, to wannan nonon yana matsayin ruwan da jariri ke buƙata ne kuma yana kawar masa da ƙishin ruwa, sannan ruwan nonon da ke ci gaba da fitowa daga mahaifiya mai kauri, shi ne yake matsayin abincin da jariri ke buƙata a rayuwarsa na ɗan wannan lokacin watanni shida kenan.

KU KUMA KARANTA: Shayar da nono zai iya ceton yara dubu ɗari a Najeriya – UNICEF

Sannan kuma! farkon nonon da ke fitowa daga ƙirjin uwa bayan ta haihu mai launin yalo yalo, wannan nonon shi yana ɗauke da wasu sinadarai masu amfani da tasiri.

Sannan kuma likitoti sun yi amanna da cewa wannan ruwan nonon yana matsayin riga kafi ne ga jariri domin kare shi daga nau’o’in cututtuka, sakamakon haka mahaifa Jarirai su tabbatar sun shayar da jariransu wannan ruwan nonon, domin yana da natuqar fa’ida, sai a jarraba a gani.

Sannan idan muka ɗauko nonon uwa, za mu ga shi ne nau’in nonon da yafi duk wani nonon da za a shayar da jariri tsabta saboda nono ne da zai zuka kai tsaye daga jikin uwa, ba kamar nonon da za’a matso daga dabba, ko nonon da ake sarrafawa daga injunonin kamfanoni, inda a wani lokaci wannan nonon zai iya cin karo da wata ƙwayar cuta kafin a kai ga shayar shi jaririn.

Tabbas a kullum nonon uwa tsabtatacce ne kuma sabon nono da baya tsufa, sabanin sauran nonon da ake sarrafawa watakila akwai tsawon lokacin da ake diba masa domin yin amfani da shi, wato da zarar ya kai wannan wa’adi to nonon ya yi expired, sannan zai iya zama guba da zai cutar da lafiyar jaririn.

Kun ga kenan nonon uwa yafi ko wane nono ba da kariya ga lafiyar Jarirai.

Leave a Reply