Wani matashi mazaunin garin Gashuwa ta jihar Yobe, mai suna Injiniya Mustapha ya ƙera injin da yake ba da ruwa, wato injin da yake zuƙo ruwa daga ‘borehole’ ba tare da wutar lantarki ko Janareto ba.
Yadda injin yake shi ne, wannan matashin Injiya ya yi amfani da wani tsohon mashin ne wajen janyo ruwan daga ‘borehole’ ta hanyar jona tsohon mashin ɗin da ‘borehole’ ɗin.
Injiniyan ya ce da tsohon mashin wanda kuɗinsa bai wuce dubu 50,000 ko 60,000 ba ake wannan aiki da shi. Ya ce idan aka saka wa mashin ɗin lita uku na man fetur, to zai yi awa 10 zuwa 12 yana aiki bai tsaya ba. Sannan bayan kwana 12 ake yiwa mashin ɗin juye.
KU KUMA KARANTA: Muhimman abubuwa 9 gameda fasahar AI (Artificial Intelligence), daga Sadiq Tukur Gwarzo
Matashin ya ce, idan aka kawo tsohon mashin ɗin, ba a cire komai a jikinsa, kawai wata dabara yake ya jona shi da borehole ɗin, daga an tayar da mashi ɗin yana ‘slow’ sai ruwa ya fara ɓulɓulowa. Garin Gashuwa dai daman an masa shaidar noman rani, na kayayyakin abinci iri daban-daban, to yanzu kuwa ga sauƙi ya samu.