Mataimakin shugaban ƙasa Shettima, ya ƙaddamar da manyan ayyuka a jihar Borno

1
323

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaddamar da sabbin makarantu uku da cibiyar kula da lafiya a matakin farko da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya aiwatar a cikin kwanaki 100 na ci gaba da wa’adinsa na biyu.

Shettima wanda ya isa Maiduguri a ranar Juma’a, ya samu tarba daga Gwamna Zulum, da shugabannin jam’iyyar APC, da manyan jami’an gwamnati a filin jirgin Muhammadu Buhari.

Sanata Shettima ya fara aikin nasa ne a makarantar Shuwari II Mega Primary School, wadda ke da ajujuwa 20 masu ɗaukar aƙalla ɗalibai 1,200.

Makarantar kuma tana da wuraren shaƙatawa na ma’aikata da wuraren wasanni.

KU KUMA KARANTA: Jihohin Borno, Adamawa, da Yobe, sun cire tallafin sufuri ga ma’aikata da ɗalibai

Haka kuma a Shuwari II, mataimakin shugaban ƙasar ya ƙaddamar da wata cibiyar kula da lafiya matakin farko mai gadaje 30, wadda aka gina domin magance ƙaruwar buƙatu na kiwon lafiya sakamakon kwararowar ‘yan gudun hijira a cikin birnin Maiduguri da kewaye.

Daga nan ne mataimakin shugaban ƙasar ya kai ziyarar ban girma ga Shehun Borno, Alhaji Dakta Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi.

Daga fadar Shehu, mataimakin shugaban ƙasar ya je ‘commissioner day Secondary School’, Gamboru, mai sunan Marigayi tsohon sakataren gwamnatin jihar Borno, Usman Jidda Shuwa.

Makarantar tana da ajujuwa 30, wuraren wasanni, da ɗakunan gwaje-gwaje, a tsakanin sauran kayan aiki.

Sannan Shettima yaje ya buɗe wata makarantar mega a unguwar Alakaramti. Makarantar tana da ajujuwa 30, shingen gudanarwa, wuraren wasanni, wutar lantarki, da tsarin ruwa.

A wuraren da aka ƙaddamar da aikin, mataimakin shugaban ƙasa ya raba riguna, kayan rubutu, da litattafai ga ɗalibai.

1 COMMENT

Leave a Reply