Masu masana’antu sun amince da ƙaddamar da katin lamunin kuɗin dala a Najeriya

0
95

Kwana biyu bayan ƙaddamar da katin lamuni na kuɗin dala a Najeriya, wato American Express Credit Card, irinsa na farko a Afrika, masana tattalin arziƙi sun fayyace bambancinsa da kuɗin Crypto, yayin da masu masana’antu ke cewa, akwai buƙatar wayar da kan ‘yan kasuwa akan alfanun aiki da katin.

A ranar Alhamis ne kamfanin American Express ya ƙaddamar da katin lamuni na kuɗin dala a birnin Legas, a wani mataki na sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya musamman ‘yan kasuwa a harkokinsu da ke da alaƙa da kuɗaɗen ƙetare na dala.

Dakta Lawan Habib Yahya, masanin tattalin arziƙi ne a Najeriya, ya yi ƙarin bayani dangane da alaƙar wannan katin na lamunin kuɗin dala da kuma darajar takardun kuɗin Najeriya na Naira.

“Idan buƙatun neman musayar kuɗaɗen ƙetare na dala suka ragu daga kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane, saboda suna samun waɗannan kuɗaɗen ta hanyar katin lamuni daga kamfanin American Express Credit Card, to babu shakka darajar naira na iya ƙaruwa saboda dama yawaitar buƙatun kuɗin dalar ne ke daga farashinta,” a cewar Dakta Lawan.

Da alama dai masu masana’antu a Najeriya sun yi maraba da wannan yunƙuri na ƙaddamar da katin lamuni na kuɗin dala a Najeriya, kamar yadda Alhaji Sani Hussaini Sale, mamba a kwamitin ƙoli na ƙungiyar masu masana’antu ta Najeriya (MAN), kuma mataimakin shugaban cibiyar kula da harkokin kasuwanci, masana’antu, ma’adinai, da ayyukan noma ta jihar Kano (KACCIMA) ya bayyana.

“Dama kokawar cinikayya da ƙasashen waje ta zama da wahala saboda dalar na neman ta tada hankali, amma zuwan wannan tsari na katin ba da lamuni na kuɗin dala zai magance ƙalubalen, musamman yadda idan aka ba ka kuɗi daga dala dubu ɗaya zuwa dubu 20 za su taimaka sosai, a cewar Alhaji Sani.

KU KUMA KARANTA:Muna ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bindiga suka sace – Gwamnatin Kogi

Ya kuma ce “Fatan mu shi ne wannan kamfani na American Express credit Card ya iso Kano a arewacin Najeriya, don mu haɗa hannu da shi a cibiyarmu. Zamu sada shi da ‘yan kasuwa domin wayar da kansu game da alfanun wannan tsari da ya zo da shi”.

Amma a cewar, Dakta Lawan Habib Yahya, akwai bambanci a tsakanin katin lamuni na American Express Credit Card da kuɗaɗen Crypto da ake hada-hadarsu a kafar zamani ta Intanet.

“Shi kuɗin Crypto kuɗi ne da ake juya shi ta kafar sadarwa ta Intanet, ba kuɗi ne lakadan ba, amma shi American Express Credit Card kudi ne lakadan za’a saka maka a katinka kuma ka yi sayayya ko cinikayya da shi a kasashen waje, kamar yadda za ka yi amfani da katinka na bankin Najeriya takardun kuɗi na naira su fita,” inji Dakta Lawan.

Baya ga Najeriya, kamfanin American Express ya ce yana da burin faɗaɗa wannan tsari na katin lamunin kuɗin dala zuwa sauran ƙasashen Afrika kamar su Rwanda da Ghana.

Leave a Reply