Rahotanni daga birnin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe, ɓarayin waya sun addabi garin, ta hanyar nuna wuƙa su ƙwaci waya, musamman a mata.
Ko a ranar Asabar da dare, masu ƙwacen sun ƙwaci waya da kuɗi a hanun wasu mata, sannan suka caka wa ɗayar wuƙa, suka gudu.
A labarin da Neptune Hausa ta samu shi ne, jiya Asabar da dare da misalin ƙarfe 9:00 na dare suka tare wasu mata a Malari Bye-Pass, suka nemi su ba su waya suka ƙi, sai suka caka wa ɗayar wuƙa suka kwashe komai suka gudu.
Matashiyar mai shekaru 24, yanzu haka ana mata magani a Asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe.
Jama’a da dama suna ta Allah wadai da wannan irin zalunci da aka mata. Hukumar ‘yan ta duƙufa wajen zaƙulo irin waɗannan matasa ɓata-gari, masu mummunar ɗabi’a.