Marainiya hafizar Alƙur’ani na son zama likita

0
502

A ranar Asabar da ta gabata ne aka yi bikin saukar karatun Alƙur’ani na Aishatu tare da abokan karatun ta, duk da cewa ita marainiya ce amma dai mahaifiyar ta data rage mata, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tsaya mata kuma bikin ya tafi kamar yadda aka shirya.

Ta ce, duk da kasancewar ta girma ba mahaifi, mahaifiyar ta da ke kula da ita ta yi ƙoƙari matuƙa domin ita ta tsaya a matsayin uwa da uba har ta sauke Alƙur’ani ta kuma kammala karatun sakandare a shekarar 2021.

KU KUMA KARANTA:Madarasatu Nuruddeen Gudau, Ta Yaye Dalibai 41 Da Su Ka Yi Saukar Alkur’ani

A cewar Aishatu duk da kasancewar ita ba ‘yar kowa ba ce mahaifiyar ta ba ta da ƙarfi hakan bai hana ta tunani zama likita ba, domin ta san idan dai karatu zai sa a zama za ta iya muddin ta samu mai tallafa wa mahaifiyar ta wajen biya mata kuɗin makaranta.

Ta kara da cewa, mahaifiyarta Malama Habiba ita ta dinga ƙara mata ƙarfin gwiwa na jajircewar wajen yin karatun, inda ta ce mata rashin uba ba hujja ba ne na ƙin yin abin da ya dace a rayuwa.

Ganin tana da ƙrancin shekaru ta samu hadda ta yi amfani da damar wajen yin kira ga mata ‘yan uwanta da cewa, su ajiye jiji da kai na ganin ni ‘yar wane ce ko ‘yar wane su nemi ilimi na addini da na zamani, domin idan da nisan kwana su ma wata rana za su zama marayu.

Aishatu Ibrahim Muhammad, ta zubar da hawaye da ta tuna yadda mahaifiyarta ta yi ɗawainiya da ita ganin cewa, ba ta da ƙarfi kuma ba ta gaza ba, a duka ɓangarorin na karatun ta da kuma hidimar gida, kuma kowa ya san yadda rayuwa ta yi tsada. Ta ce, burinta nan gaba a duniya kamar ta haddace Alkur’ani, ta fara ilimin littatafan ilimi ta samu zama likita domin ta yi wa ƙasar ta aiki ta taimaki al’umma.

Aishatu, ta nemi gwamnati ko masu hannu da shuni da ma ɗaiɗai kun mutane da su tallafa mata domin cikar burinta a rayuwa.

A nata bangaren, mahaifiyar Aishatu, Malama Habiba Idris Abubakar, da ake kira Aunty Lami, cewa ta yi, a wannan rana cike take da farin ciki na yadda Allah ya nuna mata ranar da ‘yarta ta yi bikin saukar ta na haddar Alkur’ani mai tsarki.

Malama Habiba, kullum tana ganin yadda Aishatu take karatu ba dare ba rana tana ta tilawa tana hadda ba ta bari wasa ya sha gabanta ba har ta kammala haddar Alkur’ani.

Daga nan sai ta yi addu’ar Allah ya yi mata albarka tare da sauran ‘yan uwanta, ta kuma ce, tana ci gaba da yi masu addu’a na ganin sun yi albarka, sannan kuma ta yi addu’a na musamman kan Allah ya yi wa mahaifinsu rahama ya sa yana cikin rahamar Ubangiji.

Leave a Reply