Man Fetur ɗin Ɗangote zai shiga kasuwa a makon gobe – NNPCL

0
45
Man Fetur ɗin Ɗangote zai shiga kasuwa a makon gobe – NNPCL

Man Fetur ɗin Ɗangote zai shiga kasuwa a makon gobe – NNPCL

man fetur ɗin Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa man fetur ɗin matatar Ɗangote zai fara isa kasuwa tun daga ranar 15 ga watan Satumba mai kamawa.

Kamfanin wanda ya bayyana hakan a sanarwar da babban jami’in yada labaransa, Olufemi Soneye ya fitar a jiya Alhamis a Abuja, tace kasuwa da kanta ce zata yanke farashin da za a sayar da man.

Hakan dai ya biyo bayan fara tace man fetur din da matatar ta Dangote tayi a farkon makon nan.

KU KUMA KARANTA:Nan da mako huɗu Najeriya za ta daina sayo man fetur daga waje — Ɗangote

Da yake ruwaito kalaman mataimakin shugaban bangaren cinikayyar albarkatun man kamfanin NNPCL, Adedapo Segun, Soneye yace an kammala cefanar da bangaren cinikayyar kamfanin don haka bashi da sauran hakkin yanke farashi.

Kalaman nasa sun kawo karshen rade-raden da ake yi na cewar NNPCL zai cigaba da yanke farashin albarkatun man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here