Makarantar Hafsatu Gimba Ahmad ta halarci gasar ranar makarantu masu zaman kansu ta ƙasa
Daga Ibraheem El-Tafseer
Makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial Potiskum ta halarci gasar ranar makarantu masu zaman kansu na ƙasa. An ware ranar 12 ga watan Oktoba na kowace shekara a matsayin ranar makarantu masu zaman kansu (private schools) na ƙasa, a Najeriya.
A garin Potiskum jihar Yobe, an gudanar da taron ne a filin wasa na Olusegun Obasanjo Square da ke cikin makarantar FCE (T) Potiskum. Sama da makarantu 30 ne suka halarci gasar, inda aka gudanar da gasar wasanni iri-iri daban-daban.
Wasannin sun haɗa da gudun tsere, gudun kwalba da gudun ƙwai. Sai kuma gasar fareti. Kafin nan sai da aka gudanar da gasar ‘Spelling Bee’ ga ɗalibai ‘yan firamare 4 zuwa 6.
KU KUMA KARANTA: Gidauniyar JFES ta kai tallafin takardu makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial (Hotuna)
Makarantar Hafsatu Gimba Ahmed duk da kasancewarta sabuwar makaranta, amma ta halarci taron gasar, inda ta shiga gasar tsere da fareti. Duk da kasancewar ɗaliban ‘yan Nursery da firamare ne, amma sun taka fareti gwanin ban sha’awa.
Manyan baƙi a wajen, sun haɗa da wakilin mai martaba Sarkin Fika da wakilin mai martaba Sarkin Potiskum. Sai kuma Sakataren ilimi na ƙaramar hukumar Potiskum, da sauran manyan mutane da dama daga ɓangarori daban-daban da suka halarta.