Majalisar wakilai ta yi alƙawarin ganin shugaban ƙasa ya saka hannu akan dokar mafarauta

0
243

Majalisar Wakilai ta ce za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin Fadar Shugaban ƙasa ta tabbatar da dokar nan ta Mafarauta wadda aka fi sani da “Hunters Bill” a wani mataki na ganin an samar da tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar nan.

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan Hukumomin Dutsin-Ma/Kurfi Honorabul Aminu Balele ne ya sanar da haka lokacin da shugabancin ƙungiyar ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba.

Honorabul Balele ya ce, dalilin da ya sa Majalisar Wakilai ta amince ta sake gabatar da ƙudurin duk da yake Majalisa ta 9 ta amince da ƙudurin, har ma ta tura shi ga ‘Fadar Shugaban Ƙasa’ domin a saka wa dokar hannu amma hakan bai samu ba a gwamnatin da ta gabata.

KU KUMA KARANTA: Ƙwararru sun yaba da sanya hannu akan kariyar bayanai a matsayin doka

Ya ce muhimmanci ƙudurin ne ya sa Majalisar Wakilai ta 10 ta sake dawo da ƙudurin domin ganin ya zama doka ba tare da ɓata lokaci ba.

Balele ya ƙara da cewa, Mafarauta suna da masaniya akan dukkanin dajujjukan dake ƙasarnan kuma ɓata gari sunayin amfani da dajujjuka ne wajen aikata ɓarna irin ta karɓar kuɗin fansa kuma anan ne suke ɓoyewa idan sun aikata wani laifi.

Ya ce idan an yi wannan doka za ta bawa Mafarauta dama su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami’an tsaro wajen ganin an kama masu laifi kuma an hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Honorabul Balele ya ƙara da cewa ba wani ci gaba ta zai tabbata idan babu zaman lafiya. Kamar Noma ya ce ba zai tabbata ba idan ana kashe Manoma ko kuma ana yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

Haka zalika sauran sana’o’i ma ba za su gudana ba idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali. “Shi ya sa ‘yan Majalisar Wakilai su 359 suka amince da wannan ƙuduri da na gabatar da shi a zauren Majalisa kuma tuni an miƙa ƙudurin ga Kwamiti domin ya bibiye shi” inji Honorabul Balele.

A wani ɓangaren kuma Honorabul Aminu Balele ya ce daga zuwan sa Majalisa a ƙasa da wata guda ya gabatar da ƙuduri guda 3 da kuma doka ta gaggawa guda ɗaya ba don komai ba sai don ya  sauƙe alƙawarin da ya ɗaukawa mutanen sa na samar da ƙudure–ƙudure da za su inganta rayuwar su.

Inda ya ce batun tsaro shi ne na farko sai kuma batun Noma da kuma Ilimi amma dukkannin su ba za su samu ba sai harkar tsaro ta inganta shi ya sa ya gabatar da ƙudurin Mafarauta domin sune ƙashin bayan samar da tsaro mai ɗorewa a ƙasar nan.

Tun da farko a na sa jawabin Shugaban ƙungiyar Mafarauta, Ambasada Osatimehin Joshua ya yabawa Majalisar Wakilai da ta sake karkaɗe ƙudurin domin sake gabatar da dashi a Majalisar da kuma yin gyara don ganin an sake gabatar da shi ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka masa hannu ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban Hunters ya ce dalilin su na kaiwa Honorabul Balele ziyara shi ne saboda shi ne ya gabatar da ƙudurin a gaban Majalisar. Kuma hakan ya nuna ƙarara irin kishi da yake da shi wajen ganin an samar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar nan.

Ƙungiyar ta godewa Honorabul Balele tare da nuna jin daɗinta wajen ganin Majalisar Wakilai tana goyon bayan irin gudumawar da su ke bayarwa ga al’ummar Najeriya.

Shugaban ya ƙara da cewa sanin kowa ne Mafarauta suna sadaukar da rayukan su da dokiyoyin su wajen ganin ƙasar nan ta zauna lafiya ta hanyar bawa jami’an tsaro bayanai da goyon baya a yunƙurin da gwamnati take yi na samar da tsaro a ƙasar nan.

Leave a Reply