Majalisar Tattalin Arziki ta Najeriya ta gama taro babu maganar cire tallafin man fetur

0
321

Majalisar Tattalin Arzikin ta Ƙasa a Najeriya ta kammala zamanta na farko a wannan shekarar ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ba tare da yanke shawara kan tallafin man fetur ba.

‘Yan kasar da dama sun yi tsammanin cewa a zaman ne za ta faɗi matsayinta a kan tallafin mai da ake kila-wa-kala game da dorewarsa bayan ta shawarci gwamnati ta ƙara kuɗin man zuwa N305 a watan Nuwamban 2021.

Da manema labarai suka nemi jin abin da suka tattauna, sai `yan majalisar kawai suka ɓuge da dogon bayanin mai kama da tarihi… suna cewa sun dade suna tattanauwa a kan batun, kuma sun samu bayanai masu yawa daga kwamitin da suka kafa, wanda Gwamnan Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai ya jagoranta.

Wasu daga cikin bayanan sun nuna cewa farashin litar man fetur a dukkan kasashen da suka kewaye Najeriya ya ninka farashin da ake sayarwa a cikin kasar. Kuma a bara kadai Najeriya ta kashe fiye da naira tiriliyan biyu a kan tallafin mai.

Suka ƙara da cewa ba don tallafin mai ya lashe ba, da kudi ne da za a iya amfani da shi wajen raya ilimi da samar da hanyoyin mota da asibitoci da sauran abubuwan more rayuwa.

Don haka muhawarar da majalisar ke tabkawa ita ce ko ya dace Najeriya ta ci gaba da kashe kudi fiye da samunta wajen inganta rayuwar wadanda suka mallaki abin hawa kaɗai a Najeriya?

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya faɗa wa `yan jarida cewa: “Bayan majalisar ta duba wadannan bayanan, sai ta fahimci cewa kasa da kashi daya bisa uku na jihohin Najeriya ne ke cin gajiyar kashi biyu bisa ukun tallafin man. Ka ga a nan maganar daidaito ta taso.”

Leave a Reply