Majalisar dokokin Kenya ta tsige mataimakin shugaban ƙasa
Majalisar Dokokin Kenya ta tsige Mataimakin Shugaban Ƙasa, Gachagua bisa zargin saɓa wa kundin tsarin mulki da raina gwamnati.
‘Yan majalisa 281 ne suka kada ƙuri’ar goyon bayan tsige shi, yayin da 44 suka kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa, sai ɗan majalisa ɗaya ya ƙaurace a ƙur’iar da aka kaɗa ranar Talata.
Aƙalla kaso biyu cikin uku na ‘yan majalisar – wato 233 – ake buƙata su amince da tsige Gachagua kafin matakin ya tabbata.
A yanzu za a kai batun ga Majalisar Dattijai mai mambobi 67, inda idan kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar suka bi sawun takwarorinsu na majalisar wakilai na tsige mataimakin shugaban ƙasar, to shi ke nan zai bar ofis. Sai dai Gachagua zai iya ƙalubalantar tsige shi a kotu.
Daga tuhume-tuhumen da ake yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasar, Gachagua akwai zargin tara dukiya ta da kai shillings na Kenya biliyan 5.2, kwatankawacin dalar Amurka miliyan 40.3, a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Wakilin mazabar Kibwezi ta Yamma Mwengi Mutuse, wanda ya gabatar da ƙudirin tsige Gachagua, ya ce a shekaru biyu da suka gabata, mataimakin shugaban ƙasar ya karɓi albashi na shillings miliyan 24, kwatankwacin $186,000.
KU KUMA KARANTA: Bani da hannu a sabon yunƙurin tsige Sarki Sanusi — Ganduje
Mutuse ya ƙara da cewa, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na watan Agustan 2022, Gachagua ya bayyana cewa dukiyarsa ta kai shillings miliyan 800, kwatankwacin $6.8 million.
A cewar Mutuse, akwai “ayar tambaya” kan yadda dukiyar Gachagua ta haɓaka cikin shekara biyu, yana cewa da alama an tara ta ne ta hanyar rashawa.
An zargi Mataimakin Shugaban Kasar Gachagua, mai shekaru 59 da raina gwamnati, da kuma shiga siyasar kabilanci.
Gachagua, wanda ya bayyana a majalisa ranar Talata, ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, inda ya bayyana su a matsayin “tsagwaron ƙarya.”
Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce ya samu dukiyar tasa ne daga kasuwanci daban-daban da suka hada da samar da madarar shanu, da kuma kadarar da ya gada daga marigayin ɗan’uwansa, Nderitu Gachagua.
A jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasa ranar Litinin, Mataimakin Shugaban Ƙasar, Gachagua ya ce lauyoyinsa za su shigar da ƙara a kotu, su ƙalubalanci yadda aka shigar da jama’a cikin batun na tsige shi a makon jiya.
Da yake bayyana shigar jama’a cikin batun na tsige shi, a matsayin wani “dodorido”, Gachagua ya ce matakin da aka bi “ya saɓa wa kudin tsarin mulki.”
Wasu mutanen ƙasar sun yi tsammanin Gachagua zai sanar da sauka daga kujerarsa a ranar Litinin, sai dai mataimakin shugaban ƙasar ya ce a shirye yake ya yi yaki har zuwa “inda ƙarfinsa zai ƙare” – har da shiga kotu – don tabbatar da cewa bai aikata lafin komai ba.
An zaɓi Gachagua tare da William Ruto a zaɓen shugaban ƙasar a ranar 9 ga Agusta na 2022.
Kafin nan, ya zama ɗan majalisa daga mazaɓar Mathira ta Tsakiyar Kenya tun 2017.