Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi

0
68

Ƙudirin dai ya samu amincewar rinjayen ‘yan Majalisar ta dattawa, kuma ya tsallake mataki na biyu.

Bayan doguwar muhawara da aka tafka a zauren Majalisar Dokokin Najeriya, Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin hukuncin kisa ga masu safarar muggan ƙwayoyi ko kuma ta’ammali dasu.

Ƙudirin dai ya samu amincewar rinjayen ‘yan Majalisar ta dattawa, kuma ya tsallake mataki na biyu.

Da farko dai ƙudirin dokar sashi na 11 ƙarƙashin dokar Yaƙi da sha da ta’ammali da kuma safarar muggan ƙwayoyi, (NDLEA Act) ya yi tanadin hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin shigowa, ko safarar muggan ƙwayoyi ko kuma sarrafa su.

Sai dai yanzu ‘yan Majalisar dattawan sun yiwa wannan sashi kwaskwarima, inda suka mayar da shi hukuncin kisa ga masu aikata irin wannan laifi.

Sanata Tahir Monguno, mai wakiltar Arewacin Jihar Borno, shi ne shugaban Kwamitin kula da ɓangarorin Shari’a, ‘yancin ɗan’Adam da kuma Dokoki, wanda kuma a ƙarƙashin kwamitin sa ne aka gabatar da wannan ƙudirin, duk da cewa da farko ƙudirin bayyi tanadin hukuncin kisa ga masu aikata irin laifin ba.

KU KUMA KARANTA:Majalisar dattawa ta tabbatar da Bakari a matsayin jagoran hukumar NFIU

Mai tsawatarwa a Majalisar, Sanata Ali Ndume, Sanata me wakiltar Kudancin Jihar Borno, shi ne ya bijiro da tanadin hukuncin kisa ga duk masu safarar muggan ƙwayoyi da dangoginsu, wanda daga baya ƙudirin nasa ya samu amincewar Majalisar.

A hirar ta da Muryar Amurka, Barrister Altine Ibrahim, ɗaya ce daga cikin mata masu fafutukar kare ‘yanci mata da yara, ta ce “wannan ƙudirin doka ya zo ne akan gaɓa, ganin cewa yadda yara da mata suka faɗa harkar shaye-shayen muggan ƙwayoyi”

‘Yan Najeriya dai na fatan fara ganin irin waɗannan hukunce-hukuncen a zahiri, kamar yadda suke a rubuce.

Leave a Reply