Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Alla-wadai da kashe-kashe a jihar Borno

0
35
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Alla-wadai da kashe-kashe a jihar Borno

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Alla-wadai da kashe-kashe a jihar Borno

Majalisar Dinkin Duniya ta yi allawadai da kisan kiyashin da aka yiwa farar hula na baya-bayan nan a yankin kukawa na jihar Borno, dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Sanarwar da jami’in ayyukan jin kai na majalisar a Najeriya, Muhammad Malick, ya fitar ta bayyana kisan gillar da aka bada rahoton cewar mambobin wata kungiya mai dauke da makamai ta yiwa akalla fafaren hula 40 a kauyen Dumba a ranar 12 ga watan Janairun da muke ciki, da abin tsaro da tada hankali.

KU KUMA KARANTA:Za a fuskanci yunwa mai tsanani a arewa maso gabashin Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya

An ba da rahoton cewa an hallaka mutanen da galibinsu manoma da masunta ne bayan da ake zarkin sun sabawa haramcin da kungiyar ‘yan bindigar ta sanya a kan ayyukan da suka shafi noma.

Malick ya jajantawa iyalan mutanen aka hallakan tare da yiwa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin hanzari sannan yace Majalisar Dinkin Duniyar na tare da gwamnati da al’ummar jihar Borno.

Ya kuma bukaci a gano wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar dasu gaban shari’a.

Leave a Reply