Mace ɗaya ‘tilo’ mai gyaran wayar salula a jihar Borno

3
335

Wata budurwa ‘yar asalin jihar Borno, ta zama mace ta farko mai gyaran wayar salula a fadin jihar. Matashiyar ta yi bikin yadda ta bijire wa duk wani abin da zai hana ta zama mace ɗaya tilo mai gyaran waya da sauran na’urorin fasaha. Matashiyar tana zaune ne a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Ta yi bikin tare da bayyana yadda mutane da dama a yankinsu suka dogara da aikin hannunta. Matashiyar ta samu horo ne daga kungiyar Plan International.

Plan International, wata kungiya ce mai zaman kanta ta ƙasa da ƙasa da ke mai da hankali kan inganta ‘yancin yara da daidaito ga ‘yan mata.

KU KUMA KARANTA: Abba Dalori: Injiniya ɗan Najeriya wanda ya ƙera mota mai tashi a Borno

Ta nuna jin daɗin ta ga ƙungiyar da ta ba ta horon. ‘Yan maza ne kawai suke gyara wayoyi kuma bukatar ta yi yawa a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno. Na gode wa Plan International don horar da ni da kuma tallafa mini da wasu kayan aiki kamar mita, inji, allo da sauran kayan aikin gyaran waya. Inji ta.

“Ba na aiki amma saboda zuwan kungiyar Plan International a cikin garinmu, ina da sana’a ta kaina,” in ji Falmata. Ta bayyana yadda ta jure matsi daga mutanen garinsu, waɗanda suke ganin sana’ar ba ta dace da jinsin ta ba a matsayinta na mace.

‘Ko da mutane suka yi ƙoƙarin hana ni, su sanyaya min gwiwa, na zaɓi in koyi yadda ake gyaran waya. “Yanzu zan iya gyara allon waya (screen), canza bakin magana (mouth piece) da tashar caji (charge point), zan iya yin wasu gyare-gyare kuma,” in ji ta.

Ta ce “a yanzu ina cikin farin ciki domin hatta mutanen da suke ganin ba zan iya ba, a yanzu suna kawo min aikin gyaran wayoyinsu. Wani abin da ke kara min kwarin gwiwa shi ne yadda mutane suke kawo wayoyinsu domin a gyara su,” in ji ta.

3 COMMENTS

Leave a Reply