Connect with us

Allah Ɗaya Gari Bam Bam

Mace ɗaya ‘tilo’ mai gyaran wayar salula a jihar Borno

Published

on

Wata budurwa ‘yar asalin jihar Borno, ta zama mace ta farko mai gyaran wayar salula a fadin jihar. Matashiyar ta yi bikin yadda ta bijire wa duk wani abin da zai hana ta zama mace ɗaya tilo mai gyaran waya da sauran na’urorin fasaha. Matashiyar tana zaune ne a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Ta yi bikin tare da bayyana yadda mutane da dama a yankinsu suka dogara da aikin hannunta. Matashiyar ta samu horo ne daga kungiyar Plan International.

Plan International, wata kungiya ce mai zaman kanta ta ƙasa da ƙasa da ke mai da hankali kan inganta ‘yancin yara da daidaito ga ‘yan mata.

KU KUMA KARANTA: Abba Dalori: Injiniya ɗan Najeriya wanda ya ƙera mota mai tashi a Borno

Ta nuna jin daɗin ta ga ƙungiyar da ta ba ta horon. ‘Yan maza ne kawai suke gyara wayoyi kuma bukatar ta yi yawa a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno. Na gode wa Plan International don horar da ni da kuma tallafa mini da wasu kayan aiki kamar mita, inji, allo da sauran kayan aikin gyaran waya. Inji ta.

“Ba na aiki amma saboda zuwan kungiyar Plan International a cikin garinmu, ina da sana’a ta kaina,” in ji Falmata. Ta bayyana yadda ta jure matsi daga mutanen garinsu, waɗanda suke ganin sana’ar ba ta dace da jinsin ta ba a matsayinta na mace.

‘Ko da mutane suka yi ƙoƙarin hana ni, su sanyaya min gwiwa, na zaɓi in koyi yadda ake gyaran waya. “Yanzu zan iya gyara allon waya (screen), canza bakin magana (mouth piece) da tashar caji (charge point), zan iya yin wasu gyare-gyare kuma,” in ji ta.

Ta ce “a yanzu ina cikin farin ciki domin hatta mutanen da suke ganin ba zan iya ba, a yanzu suna kawo min aikin gyaran wayoyinsu. Wani abin da ke kara min kwarin gwiwa shi ne yadda mutane suke kawo wayoyinsu domin a gyara su,” in ji ta.

3 Comments

3 Comments

  1. Pingback: Gwamna Zulum ya ƙaddamar da aikin gina gadar sama ta biyu a Borno | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Za mu gyara hanyoyin tuƙa kekuna a babban birnin tarayya Abuja – FCTA | Neptune Prime Hausa

  3. Pingback: Ko ka san amfanin jigida a jikin mace? | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Allah Ɗaya Gari Bam Bam

Na yi yunƙurin yin azumi irin na musulmai, na kusa mutuwa – Wata Kirista

Published

on

Wata matar aure mai suna Eniola Fagbemi Sisialagbo ta bayyana cewa ita Kirista ce, amma mijinta Musulmi ne, kuma tana sha’awar yadda musulmi ke azumi, domin kullum sai ta tashi lokacin sahur, ƙarfe 4:30am domin shirya wa mijin nata abincin da zai yi sahur, hakan ne ya sa ita ma wata rana ta ce za ta jaraba azumin.

Ta ce bayan ta yi sahur gari ya waye, “ƙarfe 10 na safe sai cikina ya fara amsawa, amma duk da haka na dage har zuwa ƙarfe 12 sai naga idanuna sun fara jujjuyawa, nan na ɗauki waya na ƙira mijina na sanar masa halin da nake ciki, ya ce na daure, ko da ƙarfe huɗu ta yi na suma sau biyu, sai ganin kai na na yi a asibitin SAANU da ke garin Makola a Ibadan, jihar Oyo, na rantse da Allah wannan azumi da Musulmi ke yi ba wasa ba ne, ina jinjinawa Musulmi masu Azumi.” In ji ta.

Me yasa kuke ganin ta ka sa yin azumin?

Continue Reading

Al'ajabi

Bishiyoyin da ke zubar da jini: Yadda kimiyya da gargajiya suka yarda su raba hanya

Published

on

Daga cikin abubuwa masu ban a’ajibi a hallittun tsirrai, shi ne wata bishiyar fure da aka bai wa sunan “Zuciya mai zubar da jini,” wadda ake amfani da kyawunta wajen bayyana yanayin halayyar ɗan’adam da ba a buƙata.

A yayin da wannan bishiya ba ta zubar da jini a zahiri, hotuna da bidiyo a faɗin duniya na nuna yadda wasu bishiyoyi suke fitar da wani jan ruwa kamar jini, abun da ke ci gaba da tayar da hazo kan fassararsa a gargajiyance da kimiyyance a tsakanin al’ummu.

A yankuna irin su Kudancin Amurka, ana kuskuren kallon wannan ruwa a matsayin jini, yayin da a Afirka, abin da aka fi imani da shi shi ne wai wasu mutanen ɓoye ne da ke rayuwa a cikin bishiyoyin ke fitar da jan ruwan.

A watan Oktoban 2017, masanin tsirrai ɗan ƙasar Faransa ya bayar da haske kan yadda Tepezcohuite ko “bishiya mai aman jini”, ta zama abar girmamawa a wajen jama’ar Mayas da ke kudanci Mexico zuwa Guatemala.

Wani bidiyo da aka yaɗa a yanar gizo ya tabbatar da wanzuwar irin waɗannan bishiyoyi masu zubar da ruwa kamar jini. Mene ne abin da ake muhawara a kai game da wannan jan ruwa da ke bulbulowa?

KU KUMA KARANTA: Abubuwan al’ajabi da ke tattare da dabbar ‘Batoyi’ (Hotuna)

Kimiyya ta yi watsi da wannan abi bisa cewa camfi ne kawai idan aka ce wai wannan ruwa d abishiyun ke fitarwa jini ne. Amma jama’ar Shaman da masu bin addinan gargajiya na yi wa wadannan bishiyu kallon masu tsarki.

Dr Djibril Diop, masanin muhalli kuma malami a Jami’ar Cheikh Anta Diop da ke Dakar babban birnin Senegal, ya bayyana cewa babu wata bishiya da ke aman jini ko take da wani ikon amfanarwa ko cutarwa saboda jan ruwan da take da fitarwa.

Ya nanata cewa wannan ruwa wani ɗanko ne ko ruwan cikin tsirrai danda ke taka muhimmiyar rawa wajen rayuwarsu.

Ɗankon cikin tsirrai wani ruwa ne da ke fita daga bishiya don tsaron kanta, inda ruwan cikin jijiyoyin bishiya kuma yake kasancewa fari, kuma yana fita da tsakanin gajye da reshe, wanda shi ke kai ruwa, gishiri, ko sukari ga tsirrai.

Dr Diop ya bayar da misali da bishiyar darbejiya a yankin Bandafassi take fitar da wani farin ruwa mai yawa saboda harin ciwon fungal.

“Mazauna yankin na fassara wannan da wani abin a’ajibi kan bishiyar, ba tare da sun san cewa yanayin bishiyar, yankin da take, ƙasar data fito daga ciki da kuma yanayin ciwon da za ta yi na taka rawa wajen fitar ruwan da kalarsa.

Masanin muhallin ya kuma yi nuni da cewa babu wata bishiya da ke da jini, a saboda haka a hankalce, ba za a taɓa tsammanin ta fitar da jini ba.

Ya bayar da misali da bishiyar da ake ƙira Socotra don nuni ga yadda ɗanko a reshan bishiya yake, tare da kalar jan da wasu ke tunanin ko jini ne.

Wannan bishiya da za ta iya tsayin har mita 20, na fitar da ruwa ja daya sanya har aka rubuta wasu makalolin kimiyya don bayyana ta a matsayin “bishiya mai aman jini”.

Wannan jan ruwa ya haɗa da sukari, ruwa da wasu sinadaran gina jiki, kuma a wasu al’adu ana amfani da shi wajen rini. Ana yawan alaƙanta wannan ruwa ja ga ƙarfin tace sinadarai da bishiya ke yi.

Baya ga amfani da su wajen yin rini, masana tsirrai irin su Dr Diop da masu maganin gargajiya irin su Romaric Moussounde Moussounda na da ra’ayin cewa wadannan bishiyoyi na yin magani.

Moussounda, wanda ke da fahimta kan bambance-bambancen dazukan Gabon, na da ra’ayin cewa halittu da yawa, ko nau’ikan bishiyoyi Pterocarpusda ke Afirka ko na Abitibi da ke Quebec, duk sun cancanci a yi musu kallon masu matsayi na musamman ko yin camfi game da su.

Moussounda ya na cewa “Waɗannan bishiyoyi kyauta ce daga Ubangiji da bai kamata su faɗa wani rukunin rashin tabbas ba.”

“Wannan ruwa da ke fitowa daga cikin waɗannan bishiyoyi na jini ba ne, amma kuma na da muhimmanci da matsayi irin na jini.”

Moussounda wanda ke cakuɗa gargajiyanci da zamananci a fannin kula da lafiyar zuciya da sauran ayyukan gaggawa na kula da lafiya, ya rawaito marubuci dan asalin Senegal Birago Diop, wanda a 1960 ya yi rubutu game da “Tsarkin wasu bishiyoyi”.

Moussounda ya ce “Ana yawan amfani da waɗannan bishiyu masu tsarki wajen bukukuwa da magani. Duk suna da wata alaƙa ruhaniyya ga ɗan adam.”

A yayin da masana tsirrai ke ta fashin baki kan waɗannan bishiyu masu aman jini, su kuma mabiya addinan gargajiya irin su Mayan da ke Mexico da ‘yan asalin Indiya na Barazil ko Kudancin Amurka na da ra’ayin lallai a kalli waɗannan bishiyoyi a matsayin masu tsarki ababan girmamawa.

Duk da waɗannan bambance-bambance na ra’ayi, akwai ijma’i tsakanin masana kan lallai a kare wadannan bishiyoyi, ko suna da tsarki ko babu, don kare muhalli.

Continue Reading

Allah Ɗaya Gari Bam Bam

Wani matashi ya auri mata bakwai rana ɗaya a Uganda

Published

on

Wani ɗan kasuwa, Ssaalongo Nsikonenne Habib Ssezzigu, ya auri mata bakwai a rana guda a ƙasar Uganda.

An yi bikin auren ne a ƙauyen Bugereka, a gundumar Mukono  ranar Lahadi, 10 ga Satumba, 2023.

Biyu daga cikin mata bakwai da ya aura ’yan’uwan juna ne.

An fara gudanar da aikin ne da misalin ƙarfe 8 na safe, inda aka kai Amaren ɗakin gyaran jiki domin yin salon gashi, kafin a sanya su a cikin motocin dakon kaya na Super Custom, ɗauke da faranti na musamman wanda ke ɗauke da sunayen kowace Amarya.

KU KUMA KARANTA: Mutumin da ya auri kada, ya ce zai riƙe ta cikin aminci babu cutarwa

Bayan sun yi musabaha na aure, Nsikonnene da matansa guda bakwai sun gudanar da gagarumin jerin gwano ƙarɓashin jagorancin masu tuƙa keke babura da ake ƙira “boda”, suka bi ta garuruwan Kalagi, Kasana, da Nakifuma, kafin su isa gidansu da ƙarfe shida na yamma.

An fara bikin ɗaurin auren ne da kaɗe-kaɗe a yayin da ma’auratan ke tafiya a cikin ayarin motoci, yayin da jama’a suka yi ɗafifi a bakin titi domin shaida bikin.

Wasu mutane sun ka sa gaskata cewa gaskiya ne wannan abu yana faruwa, wasu sun ce wannan shi ne karo na farko da za su halarci irin wannan taron ɗaurin aure.

Matan sun haɗa da Mariam, Madina, Aisha, Zainabu, Fatuma, Rashida, da Musanyusa, wacce ita ce matar Habib ta farko kuma tana tare da shi tsawon shekaru bakwai.

Haka Habib ya sayo sabbin motocin a matsayin kyauta ga kowane daga cikin matansa.

A wajen liyafar, an shirya kujerun angonta, kowane da sunayensu.

Nsikonnene a jawabinsa a wajen liyafar, ya yabawa matansa bisa yadda suke yi masa biyayya.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like