Ma’aikatan Najeriya Na Fuskantar Mawuyacin Hali – Shehu Sani

0
355

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana ma’aikatan Najeriya a matsayin wadanda ke cikin wani mawuyacin hali.

Kwamared Sanata Shehu Sani ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga manema labarai a filin da aka yi taron bikin ranar ma’aikata ta duniya a Kaduna.

Kwamared Shehu Sani ya ci gaba da bayanin cewa duk da matsalar matsin tattalin arzikin da jama’a ke ciki akwai wani mawuyacin halin da su kansu ma’aikatan kasar ke ciki wato dai wahala Goma da Ashirin kenan.

“Bisa ga lalacewar darajar naira da kuma tsadar kayan masarufi a kasuwa saboda haka ne ma’aikata suka taru a nan su na kokarin jaddadawa Gwamnati cewa lallai a tashi ayi wani abu mai yuwuwa game da halin da ake ciki da kuma halin da Talakawa suke ciki domin in ba a yi wannan gyara ba, to za a iya shiga cikin wani hali a kasa baki daya”.

“Kuma ganin irin yadda halin da tattalin arzikin kasa ke ciki na tabarbarewa, misali hatta wasu daga cikin manoma ba su iya zuwa Gonakinsu saboda halin tsaro, yan makaranta ba su iya zuwa makarantar saboda halin tsaro a halin yanzu an rufe jami’o’in Najeriya tsawon wata da watanni kuma Gwamnati ta kasa cimma bukatun kungiyar malaman Jami’o’i saboda haka a rana irin ta yau dole a tunatar da Gwamnati da ta tashi tsaye wajen yin wani abu kafin lamarin ya lalace baki daya.

Sanata Shehu Sani, ya kuma bayyana kwamared Ayuba Waba a matsayin wani mutum da ya cancanci Yabo da jinjina domin ya jagoranci zanga zanga a Jihar Kaduna saboda an take hakkin ma’aikata da kuma korar wasu daga aiki ga kuma wadanda aka dauka ba a biyansu Albashi don haka a kasa baki daya Ayuba Waba ya fadakar da Gwamnati sosai.

“Idan muna son canza kasar nan ya zama wajibi ya zama dole kowa ne dan Najeriya ya fito ya Sanya idanu a kan wadanda za su shugabanci wannan kasar na biyu kuma dole ne a ci gaba da wayar da kan mutane domin kada su rika yin siyasar amsar Maggi, Suga da Gishiri, idan ba haka ba ranar fita daga halin da ake ciki haka za a ci gaba da daummawa a kan mulki.”

“Idan an duba sosai za a ga cewa yan siyasa sun dawo da yaudararsu da suka saba a baya domin a baya ba su zuwa Suna, biki, saukar karatu, Jana’iza ko Coci ko wani sha’ani na masallaci. Amma a yanzu sun dawo da tsohuwar yaudarar da suka saba yi can baya don haka ya ragewa mutanen su amshi maggi, Suga da Gishiri ku kara Dora wasu kan mulki su ci gaba da taka ku su na ci maku mutunci, amma indai talakan Najeriya na neman mafita sai an nuna ba a son yin zalunci domin bayan mutum ya yi maka zalunci sau daya ko biyu ba komai amma idan an yi na uku akwai ganganci kwarai mutane su ci gaba da amincewa.”

“Kaga zababbe an Sace mutane baka ji maganar shi ba an kashe mutane baka ji maganar shi ba amma a yanzu zabe ya karato sun fara zuwa ana rabawa mutane Shinkafa don haka ayi hattara saboda abin da zai faru nan gaba ya fi na yanzu nesa ba kusa ba”, Inji Kwamared Shehu Sani.

Leave a Reply