Kusan mutane miliyan 26 a Sudan na fama da matsananciyar yunwa – MƊD
Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya, Stephane Dujarric, ya bayyana damuwa game da taɓarɓarewar yanayi na ƙarancin abinci a Sudan.
“Kusan mutane miliyan 26 da suka haɗa da maza manya, mata da yara ƙanana ne suke fama da bala’in yunwa – misali shi ne, adadin ya kai yawan mutanen Australia baki ɗaya,” in ji Dujarric, kamar yadda ya faɗa wa ‘yan jaridu.
Daga cikin mutane miliyan 26, 750,000 na dab da afkawa cikin bala’in yunwa da rashin abinci, in ji kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD).
Ya ƙara da cewa “Mutane a Sudan na fuskantar yanayi mafi muni a rayuwarsu”.
Sudan ta faɗa ƙazamin rikici inda rundunar sojin ƙasar ƙarƙashin Janar Abdul Fattah Al Burhan ke arangama da mayakan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Mohamed Hamdan Fagalo ke jagoranta.
KU KUMA KARANTA: Amurka ta ba da tallafin dala miliyan 203 don ƙarin taimakon jinƙai ga Sudan
Aƙalla mutane 12,260 ne aka kashe sannan sama da 33,000 suka jikkata a rikicin da aka fara a watan Afrilun 2023, kamar yadda alƙaluman MƊD suka bayyana.
Rikicin jinƙai na ci gaba inda kusan mutane miliyan 6.8 suka bar gidajensu tare da neman mafaka a cikin Sudan ko ƙasashe maƙota.
Ba a samu nasarar yarjeniyoyin tsagaita wuta daban-daban da Saudiyya da Amurka suka jagoranta ba da nufin kawo ƙarshen rikicin.