Connect with us

Kotu

Ku rubuta ku aje, nan bada jimawa ba kotu zata yi watsi da dokar da ta bawa mata ta sanya Hijabi a Legas – Omirhobo

Published

on

Daga Fatima Hassan GIMBA, Abuja

Biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar hakkin dalibai mata musulmai a jihar Legas na sanya Hijabi a makaranta, wani lauya dan Najeriya, Malcolm Omirhobo, ya haifar da cece-kuce ta hanyar sanya tufafin gargajiya a lokacin da ya bayyana a kotu.

A cikin wata hira da jaridar The Cable, lauyan ya yi magana ne kan salon sa tufafin da ba’a saba gani ba, da kuma abin da yake ganin kotun koli zata yi game da hukuncin da aka yanke na Hijabi.

Tambaya: Shin kana adawa da hukuncin da kotun koli ta yanke kan Hijabi saboda kuna yin wani addini daban?

Omirhobo: Ba ina magana ne kawai kan Hijabi ba, gaskiyar magana ita ce muna duban zaman lafiyar Najeriya — cewa dukkan addinai daidai suke kuma babu wani addini a hukumance, don haka bai kamata a fifita addini ba.

Tambaya: Menene zai faru idan kotun ba ta soke hukuncin da ta yanke ba?

Omirhobo: Ku rubuta ku ajiye, zasu canja shi, yanzu muka fara; za mu yi ta bin shari’ar muna da hanyoyi daban-daban, don yanzu daga karar wannan shari’ar zuwa kotun koli. Watakila ba kai tsaye ba, amma za’a sami shawarar da za ta canja wannan.

Akwai wani abu da suke kira ‘Locus standi’ a doka kafin ka kawo kara zuwa kotu, dole ne ka sami isasshen ra’ayoyi. Don haka mafi yawan lokuta musamman ma lokacin da ya shafi maslahar jama’a, idan an kawo za su jefar da shi su ce ba ka da ‘Locus standi’ kuma kai mutum ne kwalli daya kawai.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Gwamnatin tarayya ta amince da sanya hijabi a makarantun sakandare | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Kotu

Kotu a Anambara ta yanke wa tsohon ma’aikacin banki hukuncin ɗaurin shekara 121

Published

on

Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wata kotu a Jihar Anambra da ke Kudancin Najeriya ta yanke wa wani tsohon ma’aikacin banki hukuncin ɗaurin shekara 121 a gidan yari.

Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Najeriya Zagon-Ƙasa wato EFCC ce ta shigar da shi ƙara inda ta zarge shi da almundahana ta naira miliyan 112.

Mai Shari’a S.N. Odili ne ya yanke wannan hukuncin bayan ya samu Nwachukwu Placidus wanda tsohon manaja ne a bankin FCMB da laifin almundahana ta naira miliyan 112,100,000.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an gurfanar da shi ne a ranar Talata 27 ga watan Maris ɗin 2018 kan zarge-zarge 16 waɗanda suka haɗa da laifin yin jabu da sata da ƙarya.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Sai dai Mista Placidus ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa bayan an karanto masa su a kotu.

“A lokacin shari’ar, EFCC ta hanyar lauyanta Mainforce Adaka Ekwu ya gabatar da shaidu huɗu waɗanda suka bayar da takardu masu muhimmanci a matsayin hujjoji,” in ji sanarwar.

Mai shari’a Odili ya yanke wa Mista Placidus hukuncin ɗauri na shekara tara bisa zargi na biyu sai hukuncin ɗaurin shekara huɗu kan zargi na huɗu.

Sannan Mai Shari’ar ya yanke masa hukuncin ɗauri na shekara tara-tara kan zargi na biyar har zuwa na zargi na 16.

Continue Reading

Kotu

Kotu ta tsare matar da ta watsa wa mijinta ruwan zafi

Published

on

Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wata Kotun Majistire da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora a Jihar Neja, ta bayar da umarnin a tsare Amina Abashe da ake zargi da watsa wa mijinta Shehu Abdullahi tafasasshen ruwa.

‘Yan sanda sun gurfanar da wadda ake zargin ce a gaban kuliya bisa laifin yi wa mijinta mummunan rauni da ya saba wa sashe na 245 na kundin dokoki shari’a.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara, ASP Ɗanladi Marafa, ya shaida wa kotun cewa matar da ake zargi ta kwarawa mijinta ruwan zafi a sakamakon wani sabani da ya shiga tsakaninsu.

Sai dai bayan karanto ƙunshin tuhumar da ake yi wa matar da ake ƙara, ta musanta aikata laifin.

KU KUMA KARANTA: Ta zuba wa mijinta ruwan zafi saboda ta ƙi zuwa biki da ita

Lauya mai gabatar da ƙara, ya buƙaci da a tisa ƙeyar matar da ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali, domin bai wa masu ƙara damar lura da  lafiyar wanda abin ya shafa da a yanzu yake samun kulawa a Babban Asibitin Kontagora.

Ya kuma buƙaci a ɗan ba su lokacin domin  tabbatar da tsaro da kare matar da ake tuhuma.

Alƙaliyar Kotun, Khadijah Dauda, ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Afrilu.

Continue Reading

Kotu

Kisan Nafi’u: An sake gaurfanar da Hafsat Chuchu a gaban wata kotun

Published

on

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 3 ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Faruk Lawan ta sake gurfanar da matar nan Hafsat Sani Suraj da ake zargi da kisan wani hadimin gidanta mai suna Nafi’u Hafiz.

An sake gurfanar da wacce ake zargin ne bayan da aka ɗauke shari’ar daga gaban kotun Mai Shari’a Zuwaira Yusuf.

Lauyan gwamnati wanda ke gabatar da ƙara, Barista Halima Yahuza Ahmad ta shaida wa kotun cewa a ranar 21 ga watan Disamba, 2023 Hafsa Suraj ta yi amfani da wuka inda ta caccaka wa marigayin a kirjinsa da wasu sassa na jikinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Ana tuhumar Hafsat Suraj da laifin kisa, laifin da ya saɓa da sashe na 221 na kundin pinal kod.

Sai dai Hafsat wadda aka fi sani da Hafsat ChuChu ta sake yin gum da bakinta yayin da aka tambaye ta ko ta fahimci abin da takardar ƙarar ta ƙunsa.

Lauyan da ke kare ta, Barista Sani Ammani ya nemi kotun da ta bayar da umarnin gwada kwakwalwarta a Asibitin Masu Larurar Kwakwalwa na Gwamnatin Tarayya don sanin shin ko tana da lafiyar da za a iya yi mata shari’a dogaro da sashe na 278(3) na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na shekarar 2019.

Sai dai masu gabatar da ƙara sun soki roƙon na lauyan masu kariya, inda suka nemi kotun ta ɗauki wacce ake ƙara a matsayin ta musanta zargin aikata laifin.

A yayin haka kuma, kotun ta gurfanar da ƙarin mutane uku da suka haɗa da mijin Hafsat, Dayyabu Abdullahi da kuma Adamu Muhammad da Nasidi Ibrahim da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifi tare da ɓoye gaskiyar lamarin da bayar da bayanan ƙarya game da dalilin rasuwar marigayi Nafi’u.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta sa a duba ƙwaƙwalwar Hafsat Chuchu

“Waɗanda ake zargin sun yi amfani da bayanan ƙarya wajen sanar da ’yan uwan Nafi’u game da dalilin rasuwarsa inda suka ce ya rasu ne dalilin aikin basir da aka yi masa.”

Waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da shi da suka saba da sashe na 97 da 277 da 178 na kundin pinal kod.

Har ila yau, masu gabatar da ƙarar sun nemi kotun da ta cire sunan wanda ake ƙara na huɗu, wato Malam Nasidi Muhammad daga cikin jerin waɗanda ke fuskantar shari’ar.

Sai dai lauyoyin kariya, Barista Sani Ammani da Barista Haruna Magashi da Barista Fauziyya Yusuf sun yi suka kan wannan roƙon.

Lauyoyin sun ce Kwamishinan Shari’a ne kaɗai yake da wannan damar na cire sunan wani daga cikin shari’a dogaro da sashe na 124 da 125 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka.

Bayan sauraron ɓangarorin ne Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Faruk Lawan ya bayar da umarnin tsare waɗanda ake zargi a gidan gyaran hali.

Kazalika, ya ɗage sauraren shari’ar zuwa wata rana da ba a ambata ba don yanke hukunci kan batun cire sunan wanda ake zargin daga cikin shari’ar.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like