Connect with us

Doka

Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin

Published

on

Wata kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa masu wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook bulala ashirirn-ashirin tare da hukuncin biyan tara ta naira dubu ashirin kowannensu da kuma share kotun na tsawon wata guda.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ƙoƙarin ƙarin tada fitina a cikin al’umma, sannan kuma kotun ta umarcesu su koma kan dandalin na tiktok ɗin su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje haƙuri kan ɓata masa suna.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci ‘yan sanda da su binciki mawaƙan Kannywood, Safara’u, Ado Gwanja, da sauransu

Matasan, Mubarak Isa Muhammad da aka fi sani da Mu, da Nazifi Muhammad Bala, na shirya gajeren bidiyon barkwanci, inda akasari suke kwaikwayon muryoyin wasu fitattun mutane.

Mabarak Unique Pidkin da abokinsa za kuma su share harabar kotun Norman Silance baki dayanta har na tsawon wata guda.

Lauyan da ya shigar da ƙara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa BBC cewa, na gurfanar da matasan ne a gaban kotun saboda laifukan da suka haɗa da ɓata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma ƙoƙarin tayar da fitina,

Inda kuma suka amsa laifinsu al’amarin da yasa aka yanke musu hukuncin, Lauya mai gabatar da ƙara ya ce an kama matasan tun makon jiya inda aka gurfanar da su a gaban kotun, kafin daga bisani kuma aka aika su gidan yari.

Matasan dai suna hannun jami’an tsaro har sai sun cika waɗannan ƙa’idu kafin a sakesu.

Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci shi ne lauyan matasan, ya kuma gode wa kotun majistaren bisa sassaucin da ta yi musu game da hukuncin, don haka ma basu ƙalubalanci hukuncin ba.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Yadda ’yan sanda suka kama Murja ‘yar tiktok a Otal | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Doka

Kotu ta umarci jihar Ondo da ta biya diyyar naira miliyan 30 ga mutumin da ‘yan Amotekun suka harbe

Published

on

Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wata babbar kotun Ondo da ke zamanta a Akure, a ranar Larabar da ta gabata ta umarci gwamnatin jihar Ondo da ta biya wani Oluwasegun Oluwarotimi kuɗi naira miliyan 30 a matsayin diyyar harbin bindiga da ya samu a wata arangama da jami’an tsaro na jihar, wanda aka fi sani da ‘yan Amotekun.

Oluwarotimi mai shekaru 36, mai tuƙa babur ne, wato ɗan okada ne lokacin da lamarin ya faru.

A nasa jawabin, Mai shari’a Adejumo ya bayar da umarnin a biya Oluwarotimi kuɗi naira miliyan talatin a matsayin diyya.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NYSC ta biya diyya ga dangin ɗan bautar ƙasa da ya ɓata

Oluwarotimi, wanda a yanzu an yanke shi ne sakamakon harbin da aka yi masa ba bisa ka’ida ba,inda ya shigar da karar a gaban kotu.

“B bisa ka’ida ba a titin Araromi a ranar 9 ga watan Agustan 2021 a Akure, harbin da Amotekun ta yi ya saɓa wa hakkin ɗan Adam.

“Kotu ta umurci waɗanda ake ƙara da su hada kai su biya Naira miliyan 20 ga wanda ake kara a matsayin diyya na gaba daya da kuma Naira miliyan 10 a matsayin diyya ta misali,” in ji alkalin.

Continue Reading

Doka

An sanya dokar hana fita a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar ta-ɓaci har zuwa faɗuwar rana don kaucewa taɓarɓarewar doka da oda, biyo bayan tattara sakamakon zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin.

KU KUMA KARANTA: Yadda Abba Kabir Yusuf na NNPP ya lashe zaɓen Kano

Ya ce an yanke shawarar ne don hana ’yan daba su haifar da hargitsi a halin da ake ciki.

Kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar da su kasance a cikin gida domin jami’an tsaro ba za su ƙyale kowa ko wata ƙungiyar da ke da niyyar haddasa fitina ba.

Continue Reading

Doka

Kotu ta sanya sharudɗa akan batun bada belin doguwa

Published

on

sharudɗan sune kamar haka:

Kotu ta haramtawa Alhassan Ado Doguwa zuwa mazaɓarsa ranar zaɓen ta gwamna da ‘yan majalisar jiha.

Wannan dai na cikin sharudɗa da babbar kotun tarayya ta sanya kafin bada belin Alhassan Ado Doguwa.

Ga dai ƙarin jerin sharudɗan da kotu ta sanya kafin bada belin.

1- Zai ajiye zunzurutun kuɗi har naira miliyan 500

2- Gabatar da sarki mai daraja ta ɗaya a matsayin wanda zai tsaya mishi.

KU KUMA KARANTA: INEC ta cire sunan shugaban masu rinjaye, Doguwa daga jerin sunayen ‘yan majalisar wakilai

3- Gabatar da babban sakatare a gwamnatin jiha ko ta tarayya a matsayin wanda zai tsaya mishi.

4- Zai ajiye Fasfo da sauran dukkanin takaddunshi na tafiya a kotu.

A karshe kuma kotu tace bazai halacci mazaɓarsa ba yayin zaɓen gwamna da yan majalisun jiha dake tafe.

Ko ya kuke kallon wannan batu?

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like