Kotu ta umarci ‘yan sanda da su binciki mawaƙan Kannywood, Safara’u, Ado Gwanja, da sauransu

2
327

Daga Fatima GIMBA Abuja

Kotun Shari’a ta Jihar Kano ta Bichi ta umurci rundunar ‘yan sandan Kano da ta ƙaddamar da bincike kan Mr 442, Safiyya Yusuf (Safara’u), Ado Gwanja da wasu mutane bakwai.

Ado Gwanja da safara’u

Neptune Prime ta samo rahoton cewa wannan yana ƙunshe ne a cikin takardar koke da kotu ta aika da umarni a watan 30 ga Agusta, 2022.

Amude Booth

Sauran waɗanda suke cikin takardar koken sun haɗa da, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Murja Ibrahim, Ummi Shakira, Samha M Inuwa da Babiyana.

Kawu Ɗan Sarki

Lauyoyi 9 ne suka rubuta takardar koke inda suka roƙi kotun da ta ba da umarnin gudanar da bincike kan mawaƙan.

murja Tiktok

Idan dai za a iya tunawa dai a kwanakin baya Ado Gwanja ya fitar da wata sabuwar waka mai suna ‘Asosa’ wacce ta haifar da cece-kuce da tofin Allah tsine.

2 COMMENTS

Leave a Reply