Yadda Attajiri ya rasa dukiyarsa ya zama mai ga ruwa saboda rikicin boko Haram

2
384

Malam Isa Ibrahim, ɗan asalin garin Wudil ne da ke ƙaramar hukumar Wudil a jihar Kano. Yanada mata biyu da ‘ya’ya bakwai , maza hudu mata uku.

Kasancewarsa manomin rani, ya bar garin Wudil zuwa Baga da ke jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya, inda ya je yin ci rani a ƙarshen shekarar 1990, ya kuma gwanance a noman albasa da masara.

Yayinda malam Isa ya zama mai garuwa

Malam Isa ya mallaki fili kusan hekta biyar inda ya fara noma, da farko dai albasa yake nomawa, sannan daga baya ya yanke shawarar haɗawa da masara.

Dayake Allah Ya bashi sa’a, ya sami damar girbin albasa fiye da buhu 100 da buhunan masara kusan 100, wannan ya zamar masa al’ada na shekara da shekaru inda duk shekara yake samar da kwatankwacin haka koma fiye da hakan.

Malam Isa ya samu damar siyan injin famfo guda biyu kowanne akan kuɗi naira 27,000.00 bayan ya kwashe shekara yana ɗaukar aiki sannan kuma ya sayi babur guda biyu kowanne akan kuɗi naira 115,000 domin sauƙaka zirga-zirga, ya samu nasara sosai a harkar noma, ya sayi fili inda ya yi wa kansa da iyalinsa gini.

Da yake bayar da labarinsa, mutumin da a yanzu ya koma sana’ar sayar da ruwan ya ce,
“Ban taɓa ganin ko jin labarin wani yanki na kasuwanci a yankin Arewa maso Gabas inda ake karɓar haraji a kullum da maƙudan kuɗaɗe kamar na yankin Baga ba, Muna biyan haraji kan kowane amfanin gona da ake nomawa, haka ma masu kamun kifi”.

Ya ce, baya ga biyan bukatun iyalansa, yana kuma taimaka wa mabuƙata ba tare da la’akari da su waye da kuma inda suka fito ba, yana kuma jan hankalin mutane wajen share hawayen idonuwan jama’a.

Malan Isa

Duk da ɓarnar Boko Haram a Borno, musamman a yankin Baga, amfanin gonarsa na cigaba da samun albarkatu masu yawa, da kuma kawo kuɗaɗen shiga. Malam Isa ya bayyana cewa, yayin da ayyukan Boko Haram ke ƙara ta’azzara, haɗarin zuwa gona ya ƙaru domin ana iya kashe mutum idan aka ci karo da ‘yan Boko Haram a gonar.

Ya kan ga an yanka gawarwakin mutanen da suka san su sosai, duk lokacin da ya fita gona, da farko tsoro ya kama shi kuma a hankali ya shiga sai ya saba ya fara jurewa, yayin da yake ci gaba da bayyana munanan abubuwan da ya faru, ya ce, ranar farko da Boko Haram suka ƙaddamar da harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 42, na ɗaya daga cikin munanan ranaku da ba zai taba mantawa da su ba.

A ranar ne ya ga gawawwaki kamar bala’i, ba wai gani kawai ba, yana daga cikin waɗanda suke ɗibar gawarwakin da kuma shirya su domin binnesu.

Ya ƙara da cewa, da farko ya yanke shawarar ɗaukar iyalinsa ya bar Baga, duk da albasar da aka dasa, amma bayan tunani na biyu, sai ya yanke shawarar ya ci gaba da gudanar da harkokin noma, ya sani sarai cewa Allah ne wanda yake kare mu daga cutarwa a koda yaushe.

Malam Isa ya ƙara da cewa, “Muna gudu cikin daji domin tsira a duk lokacin da aka kai hari kuma wannan lamarin, ba zai iya ƙirguwa ba, ya ce, ’yan uwansa ma sun kasance waɗanda abin ya shafa, yan Boko Haram sun same shi tare da ɗansa a gonarsa, inda suka yanka su kamar raguna.”

Ya kuma ƙara da cewa, rayuwa ta kara shiga cikin haɗari da damuwa, ta yadda dole ne su kula da tsaron al’ummarsu ta hanyar yin gadi da daddare, tare da sanya kansu a cikin lunguna na garin, kawai don ceto da kare rayuwarsu dana iyalai ba tare da wata hukumar tsaro a kusa ba.

Ya ce, yayin da ta’addancin ke ƙaruwa da kuma rashin sojoji, an kashe rayuka da dama, ciki har da hakimin ƙauyen.

’Yan Boko Haram su kan zo su karɓi haraji , a kan miliyoyin Naira wasu kuma na dubbai. rashin yin haka, hukuncin kisa ne.
Tsoro ya fara kama ni gaba daya, kuma tsaron iyalina ya zama na farko, amma yadda za a kwashe su daga Baga matsala ce babba, domin idan Boko Haram sun gano haka, mutum na shirin fita, mutum ya zama marigayi.

Malam Isa ya ƙara da cewa “duk da tashe tashen hankulan, har yanzu harkokin kasuwanci na ci gaba da gudana duk da cewa ba kamar yadda ake yi ba a baya.

Yawancin mutane suna zuwa daga Maiduguri don siyan kayan amfanin gona da kifi, wannan ya zama wata babbar dama a gare shi na barin garin, amma adadin mutanen gidansa (matansa 2, ‘ya’yansa 7 da jikoki 3, ciki har da kansa, wannan ba zai yiwu ba a lokaci guda.

Ya ce, “Hikima na da matuƙar muhimmanci, domin wannan babbar mutum zai iya faɗawa cikin matsala babba, idan ‘yan Boko Haram suka gano hakan, sukan ƙyale tafiya amma ba kaya.”

A haka ne ya fara tura iyalinsa kaɗan da kaɗan, da sunan zuwa Maiduguri siyayya, daga nan sai su sami hanyar komawa gida, wasu suka nufi Wudil wasu kuma Potiskum kamar yadda aka tsara.

Ya kuma bayyana cewa, “babu wata hanyar sadarwa ta wayar salula da mutum zai iya kira domin sanin lafiyarsu. Ni kaɗai aka bar ni da ɗana wanda ya yi aure daga Matile, wani gari kusa da Baga.”

Ya ci gaba da ayyukan noma kuma kamar yadda aka ambata a baya, yakan sami girbi mai yawa, duk da cewa shi manomi ne mai karamin jari a lokacin, amma duk shekara yana sayar da buhunan albasa sama da 100 da kuma buhunan masara sama da 100 kuma a madadin hakan, “Ina samun sama da Naira miliyan biyu (N2,000,000.00)”, a cewarsa shi.

Ƙara kai hare-haren Boko Haram ya sa ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya fita shi ma, kuma yanayin rashin ɗaukar kaya a yayin tafiya ya sa ya fice ya bar jarinsa na miliyoyin Naira.” Malam Isa ya ci gaba da cewa, “Duk da albasar ta kusa girbi, masara kuma tana bunqasa, da hawaye a zuciyata, na kalli gonar na ce “Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi, sannan na tafi.

Hakan ya kasance a cikin 2013.” Ya ce, “Na fara sabuwar rayuwa a garin Potiskum na jihar Yobe, tare da matata ta biyu wacce ‘yar kabilar Bolewa ce da ‘ya’yana uku. Yayin da matata ta farko da ‘ya’yana huɗu suke zaune a Wudil, garinmu.”

Rayuwa ta zama mai wahala sosai, domin yadda zai faro abin babban lamari ne a gare shi kuma matansa biyu dole haka suka haƙura suka zauna a gidan iyayensu. “Tunanin yadda zan fara hidimar su, da kuma ta ina ya kamata na fara ya dameni. Na bar duk abin da na mallaka a Baga,” Malam Isa ya bayyana.

Ya ci gaba da bayyana cewa, akwai lokacin da aka ba su katin tikitin karɓar kayan abinci a sakatariyar ƙaramar hukumar Potiskum, ya haɗa har na tsawon shekaru biyu, amma tun daga lokacin, har zuwa lokacin cika wannan rahoto, bai iya samun taimako ba.

Malam Isa cikin karfin hali ya ce, “Ba kamar wasu da muke hali ɗaya ba, kuma suka yanke hukuncin yin roƙo, na yanke shawarar neman aikin da zan yi don biyan bukatun iyalina.
“Ni ba malalaci ba ne, wasu lokutan za a kira ni in raba itace ta hanyar amfani da gatari, wani lokacin kuma, in je in yi aiki a gonakin wasu yayin da ake biyana albashi. “

“Wata rana wani mai sayar da ruwa ya gaya mani cewa, zai yi tafiya ya tambaye ni ko zan iya amfani da keken kurar sa kafin ya dawo, sai na amsa da ‘eh zan iya’ sai na karɓo keken. Ya fara da kai galan biyar, tun da bai saba ba, daganan sai ya koma galan takwas, sannan a ƙarshe ya kan kai galan goma sha biyu.

Bayan wani lokaci sai mutumin da ya ara masa keken sa ya dawo daga tafiyarsa yana neman kekensa ya tambaya. Malam Isa ya tambaya ko zai iya taimaka masa ya samu wani kuma ya yi sa’a ya samu na haya.

Tun daga lokacin ya maida hankali ne kan sana’ar sayar da ruwa kuma shekara ta bakwai kenan, amma, da ƙyar yake samun Naira dubu ɗaya a rana wanda bai kai Naira 350,000.00 a shekara ba idan aka kwatanta da lokacin da yake Baga yana samun sama da N2,000,000.00. a shekara, a gonarsa.

A matsayinsa na wanda ya taɓa rikewa da sarrafa jarin da ya kai miliyoyin Naira, sam hakan bai zo masa da sauƙi ba,

“Na yi imani cewa Allah ne a kan komai, kuma ba ni da wani zaɓi da ya wuce in karɓa hakan a matsayin jarrabawa ga Allah”, ya yi bayani cike da ikhlasi.

Ya ce, idan har zai samu abin da zai koma ya ci gaba da noma, ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin hakan. Hanyoyin sun haɗa da Jari, filin noma, kayan aikin gona da wurin kwana, amma zai fi son sauyin yanayi, musamman Ngalda a ƙaramar hukumar Fika ta Yobe ko Gashua.

Ya ce duk da wannan, bai bar abin da ya same shi ya chanza masa halayya ba. Har yanzu yana iya bada ɗan abin da yake da shi ga waɗanda ke buƙata kamar yadda ya saba yi lokacin da yake garin Baga.

Ya ƙarƙare da cewa “Ina godiya ga Allah da halin da na tsinci kaina a ciki, kuma na san wata rana labarin zai sake canzawa”

Daga Omale John Achimugu

Fassara: Neptune Hausa

2 COMMENTS

Leave a Reply