Kamfanin NNPCL ya cim ma yarjejeniya ta shekara 10 da Ɗangote
Kamfanin mai na NNPCL ya cim ma yarjejeniya da kamfanin mai na Ɗangote inda NNPCL in zai rinƙa samar da gas ga Dangote tsawon shekara goma.
Sashen harkokin gas na kamfanin NNPCL wato NGML ne ya ƙulla yarjejeniyar da Dangote a ranar Laraba inda zai rinƙa bai wa Ɗangoten cubic feet miliyan 100 na gas a kowace rana na tsawon shekara 10.
Kamfanin na NNPCL ɗin ya sanar da cewa Ɗangoten zai yi amfani da gas ɗin domin samar da wutar lantarki da kuma aiki da shi a matatarsa.
Yarjejeniyar da suka ƙulla ta shekara goma ce kuma a ƙarƙashinta akwai damar Ɗangoten ya buƙaci ƙarin gas daga NNPCL ko kuma tsawaita yarjejeniyar bayan shekara goma.
Kamfanin na NNPCL ɗin ya bayyana cewa wannan yarjejeniyar ta kasance wani muhimmin mataki na tabbatar da nasarar aikin matatar man Ɗangote da kuma inganta amfani da iskar gas a cikin Nijeriya.
A ‘yan kwanakin nan an ta samun rashin jituwa tsakanin kamfanin na NNPCL da kuma Ɗangote dangane da abubuwa da dama waɗanda suka shafi jigilar man fetur da farashin man fetur da sauransu.
KU KUMA KARANTA: Mu bai wa matatar Ɗangote goyon baya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa; Shugaban IPMAN
Haka kuma an ta samun kwan-gaba-kwan-baya tsakanin kamfanin na Ɗangote da kuma ‘yan kasuwa masu dakon man fetur dangane da yadda za su sayi mai da kuma dakonsa.