Janye takunkumin ECOWAS: An dawo da wutar lantarki a Nijar

0
80

Najeriya ta amince da dawo da hasken wutar lantarki ga jamhuriyar Nijar bayan janye wasu takunkumai da ‘Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙi Ƙasashen Afrika ta Yamma’ (ECOWAS), ta yi kan ƙasar.

An ɗage wasu takunkuman ne bayan wani taron ƙungiyar na musamman kan zaman lafiya da siyasa da kuma yanayin tsaro a yankin ƙasashen ECOWAS a ranar Asabar a Abuja.

Tun watan Agustan bara, Najeriya ta katse wutar lantarki a Nijar bayan juyin mulkin soja da ya hamɓarar da shugaba Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki.

Wannan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙarshen watan Yulin bara, ya fusata shugabannin ƙungiyar ECOWAS, inda suka yi barazaanr ɗaukan matakin soji a kan ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Al’ummar Nijar na maraba da matakin ECOWAS na janye musu takunkumi

Amma daga bisani ECOWAS ta ƙaƙaba takunkumai kan Nijar, domin matsa mata lamba don maida ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya cikin gaggawa tare da sakin shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa da sauran waɗanda suke tsare da aka kama yayin juyin mulkin.

Buƙatar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi na a janye takunkuman biyo bayan ƙiran da tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Yakubu Gowon ya yi, wanda hakan ya taimaka wajen saurin ɗaukar matakin ECOWAS na neman dawo da ƙasashen uku na yankin da sojoji su ka ƙwace mulki.

Al’ummar Nijar da musamman ‘yan uwan su a arewacin Najeriya sun yi farin cikin matakin dawo da hasken wutar da rashinta ya jefa talakawa da dama cikin wahalhalun neman makamashi.

Leave a Reply