Janar Tchiani ya zama shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar Nijar na shekara 5
Daga Idris Umar, Zariya
An rantsar da Janar Abdouramane Tchiani a matsayin shugaban riƙo na Jamhuriyar Nijar, wanda zai kwashe shekara biyar yana jan ragamar Gwamnati kafin miƙa mulki.
Hakan wani ɓangare ne na aiwatar da rahoton babban taron ƙasar da aka yi a watan Fabairun da ya gabata.
A lokacin bikin rantsuwar a ranar yau Laraba, shugaba Abdourahmane Tchiani ya kuma zama janar ɗin soja mai tauraro biyar, wanda hakan na daga cikin shawarar taron ƙasar.
Bikin rantsarwar da aka yi a babban ɗakin taro da ke cikin birnin Yamai ya samu halartar sojoji, tsaffin shugabanin kasar Sallou Djibo, Mammane Osoumane, Muhammed Issoufou da kuma manyan masu ruwa da tsaki na ƙasar.
Kafin shan rantsuwar na yau, janar Tchiani ya kasance shugaban majalisar ceton ƙasa, wadda aka kafa tun bayan kifar da gwamnatin Malam Muhammed Bazoum wanda yanzu haka ake cigaba da tsareshi a fadar gwamnatin Kasar
Wane ne Janar Tchiani?
Janar Abdourahmane Tchiani wanda ya taɓa shiga aikin wanzar da zaman lafiya a ƙasashe da yaƙi ya ɗaiɗaita, shi ne ya jagoranci juyin mulkin da ya hamɓarar da shugaban ƙasar Mohamed Bazoum shekarar 2023.
Janar ɗin wanda ba sananne ba ne a wajen mahaifarsa, ya kasance kwamandan dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa kafin ya taso ya hamɓarar da mutumin da aka ɗora masa alhakin tsarewa.
KU KUMA KARANTA:Mulkin soja ya fi mana alheri a kan Dimokuraɗiyya – ‘Yan Nijar Mazauna Najeriya
Janar Tchiani ya ayyana kansa Shugaban Kungiyar Ceton Ƙasar, wanda suka kasance shugabanni da aka kafa bayan kwace iko a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
A tsawon shekaru 40 da ya ɗauka yana aikin soji, Janar Tchiani ya samu horo a ƙasashen Senegal, Faransa, Moroko, Mali da kuma kasar Amurka.
Ya kuma yi aiki a:
Ya yi aiki a matsayin jami’in wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Ivory Coast da yankin Darfur na Sudan da kuma Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Ya shiga cikin tawagar Ecowas da aka tura Ivory Coast
Ya kuma yi aiki cikin dakarun haɗin gwiwa na ƙasashen waje, inda dakaru daga Nijar, Chadi, Najeriya da kuma Kamaru suka haɗa kai wajen yaki da ƴan kungiyar Boko Haram.
Janar Tchiani ya kuma jagoranci rundunoni daban-daban a Nijar, duk da cewa ba wanda ke yaki da masu iƙirarin jihadi ba.
Sai dai abubuwa biyu ne aka fi tunawa da su game da shi a tsawon rayuwarsa ta aikin soji.
Kafin kara masa matsayi zuwa mai jagorantar dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa a 2011, bai taɓa riƙe wani babban muƙami ba a ciki da wajen ƙasar wanda ke buƙatar aiki da shugabannin gwamnati da masu haɗin gwiwa na ƙasashen waje.
Janar Tchiani mai shekra 64 ya kasance babban jami’in soja da ake ɗora wa alhakin gudanar da wasu ayyuka na musamman maimakon jagorantar ɓangaren tsaro.
Ko da bayan naɗa shi shugaban dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa da tsohon shugaban ƙasar Nijar Mahamadou Issoufou ya yi, bai cika fitowa ya yi magana ba kan abubuwan da ke faruwa.
Ba ya cikin tattaunawar jin ra’ayin jama’a da aka yi na hanyar da za a bi wajen daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi da kuma rikice-rikice tsakanin al’umma da ke yi wa mutane barazana a tsawon shekaru.