Jami’ar Kwara ta rage wa ɗalibai masu buƙata ta musamman kuɗin makaranta
Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) ta sanar da rage Naira 100,000 na kuɗin makaranta ga ɗalibai masu bukata ta musamman.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shaykh-Luqman Jimoh ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da muƙaddashin daraktar hulɗa da jami’ar, Dr. Saidat Aliyu ta fitar.
Hakazalika, ya ce jami’ar tana aiwatar da tallafin Naira 50,000 kowane wata ga ma’aikatan jami’ar masu fama da buƙata ta musamman tare da ƙarin guraben aikin yi ga masa a fannin koyarwa na masu buƙata ta musamman.
KU KUMA KARANTA: Matatar mai na Ɗangote ya rage farashin fetur ɗinsa
Jimoh ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani taron da aka shirya don bikin ranar masu buƙata ta musamman ta duniya ta 2024 a ofishin tallafawa nakasassu na jami’ar da ke Sashen Ilimi na Musamman.