Jami’an tsaro sun halaka ƴan bindiga da ƙwace makamansu da babura a Kaduna

1
534

Jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama a wani samame da suka kai a yankin Galbi da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce rundunar Operation Forest Sanity tare da haɗin gwiwar sojojin sama suka far wa matattarar ƴan bindiga a yankin na Galbi.

kU KUMA KARANTA: ‘Yan Ansaru nata ɗaura aure da ‘yan mata a Jihar Kaduna

Duk da cewa kwamishinan bai bayyana adadin ƴan bindigan da aka kashe ba, amma ya ce dakarun sun samu nasarar ƙwace bindigogi masu sarrafa kan su guda biyu da kuma AK47 guda uku da babura bakwai.

Ya bayyana cewa tun da farko dakarun sun tsallaka Kogin Kaduna inda suka rinƙa musayar wuta da ƴan bindigan, bayan haka ne suka samu kashe da dama daga cikinsu.
Gwamnatin ta Kaduna ta gode wa sojojin ƙasa da na sama da ƴan sanda da jami’an tattara bayanan sirri da ƴan bijilanti da waɗanda suka taimaka wurin samun wannan nasara.

Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin da ƴan bindiga suke cin karen su babu babbaka musamman yankin Birnin Gwari da Chikun da ke jihar.

Sai dai a baya-bayan nan gwamnati ta ce tana samun nasara a kan ƴan bindigan, domin ko a kwanakin baya sai da sojojin sama suka ce sun kashe wani ƙasurgumi kuma jagoran ‘yan fashin daji da ke ayyukansa a Jihar Kaduna mai suna Alhaji Shanono tare da yaransa 17.

Sai dai bayanai daga yankunan Birnin Gwari da Giwa kuwa na cewa har yanzu akwai mayaƙan Ansaru da ke ikirarin jihadi da addabar yankunan inda ko a kwanakin baya sai da aka samu rahoton yadda mayakan na Ansaru ke auren ‘yanmatan a yankin.

1 COMMENT

Leave a Reply