Jami’an Amotekun a Ondo sun kama ƴan arewa 168 da suka ɓuya a ƙarƙashin shanu

0
549

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Jami’an tsaro masu zaman kansu a jihar Ondo, waɗanda aka fi sani da Amotekun sun tsare wasu mutane 168 da ake zargi da kutse a cikin manyan motoci biyu.


Wannan ya zo ne bayan kwanaki uku da kama wasu mutum 151 da su ma ake zargi da kutse cikin jihar, ɗauke da layu a buhunhunan shinkafa a yankin Sango da ke babban titin Akure-Ado.

Kwamandan jami’an Akogun Adetunji Adeleye ya ce an tare waɗanda ake zargin ne a kusa da al’ummomin Itaogbolu da Iju da ke karamar hukumar Akure ta arewa yayin da ake binciken motoci.


Kamar yadda kwamandan ya bayyana, mutanen da aka kama sun zo ne daga jihohin Kano da Jigawa ba tare da tabbacin me ya kai su jihar Ondo ba.

Leave a Reply