Hukumar ‘Yan sandan Najeriya ta kori jami’in ta dayayi zalunci

1
333

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Hukumar ƴan sandan Najeriya ta kori ɗaya daga cikin ma’aikatanta saboda cin zalin wani farar hula.
Jami’in mai suna Liyomo Okai da ke aiki a babban ofishin ƴan sanda na Ekori a Jihar Rivers, an gan shi ne a wani bidiyo na ranar 31 ga watan Yuli yana dukan wani mutum da adda.


Rundunar ƴan sandan ta sanar da hakan ne a shafinta na Tuwita a jiya da yamma. Ta kuma ce korar jami’in ta fara aiki nan take daga ranar 8 ga watan Agusta.


Sifeto Janar na ƴan sanda IGP Usman Alkali Baba psc(+), NPM, fdc, ya bayyana matukar takaicinsa akan rahoton cin zali da ƙwace da ake tuhumar wasu ƴan sanda a ƙorafe-ƙorafen da jama’a suka gabatar a kafafe daban daban da aka gabatar, har da waɗanda ake yi a shafukan sada zumunta.


Babban sufeton ƴan sandan ya kuma bai wa duka kwamishinonin hukumar umarnin tabbatar da sa ido sosai da kula da ayyukan jami’anta kan faruwar irin waɗannan abubuwa.

1 COMMENT

Leave a Reply