Sojojin Najeriya sun kama masu kai wa ‘yan Boko haram kaya da abinci

0
341

Sojojin Najeriya na bataliya ta 195 sun ce sun kama mutane bakwai masu jigilar kai wa mayaƙan Boko Haram da masu satar mutane kayayyaki.

Hukumomin sojin sun ce sun yi nasarar kama mutanen ne da suka hada da Hadiza Ali da Kelo Abba da Mariam Aji da Kamsilum Ali da Ngubdo Modu da Abiso Lawan da wasu, a wajen babban birnin jihar Borno, Maiduguri.

Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa wannan na ƙunshe ne a wasu bayanan sirri da wani masanin harkokin tsaro Zagazola Makama, ya samu tare da bayyanawa jaridar.

Rahoton ya nuna cewa an kama mutanen ne da tarin kayayyaki da suka hada da man fetur da gidan sauro da taliya a yayin wani bincike, a kan hanyarsu ta kai wa ‘yan Boko Haram kayayyakin.

”Sojojin sun zargi mutanen ne bayan da suka ga garin-kwaki mai yawan gaske an ɓoye a cikin galan-galan da kuma ƙarƙashin motar da mutanen ke ciki.” kamar yadda rahoton ya nuna.

Ya ƙara da cewa, ” Bayan an tsananta bincike ne sai matan suka tabbatar wa da sojojin cewa su ‘yan Boko Haram ne da ke aiki a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Garejin Muna da Mafa da Dikwa, inda mayaƙan ke zaune a yankin bakin ruwa na Boboshe da Gulumba a karamar hukumar Dikwa ta jihar ta Borno.

A sanadiyyar wannan kamen ne kamar yadda bayanan suka nuna sojojin suka fadada bincike abin da ya kai su ga kashe dan Boko Haram ɗaya da ƙona wata babbar mota ɗaya suka kuma kuɓutar da mutum biyar da aka sace a wani sansani.

Leave a Reply