Hukumar ‘Yan sandan Najeriya ta kori jami’in ta dayayi zalunci

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Hukumar ƴan sandan Najeriya ta kori ɗaya daga cikin ma’aikatanta saboda cin zalin wani farar hula.
Jami’in mai suna Liyomo Okai da ke aiki a babban ofishin ƴan sanda na Ekori a Jihar Rivers, an gan shi ne a wani bidiyo na ranar 31 ga watan Yuli yana dukan wani mutum da adda.


Rundunar ƴan sandan ta sanar da hakan ne a shafinta na Tuwita a jiya da yamma. Ta kuma ce korar jami’in ta fara aiki nan take daga ranar 8 ga watan Agusta.


Sifeto Janar na ƴan sanda IGP Usman Alkali Baba psc(+), NPM, fdc, ya bayyana matukar takaicinsa akan rahoton cin zali da ƙwace da ake tuhumar wasu ƴan sanda a ƙorafe-ƙorafen da jama’a suka gabatar a kafafe daban daban da aka gabatar, har da waɗanda ake yi a shafukan sada zumunta.


Babban sufeton ƴan sandan ya kuma bai wa duka kwamishinonin hukumar umarnin tabbatar da sa ido sosai da kula da ayyukan jami’anta kan faruwar irin waɗannan abubuwa.


Comments

One response to “Hukumar ‘Yan sandan Najeriya ta kori jami’in ta dayayi zalunci”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Hukumar ‘Yan sandan Najeriya ta kori jami’in ta dayayi zalunci […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *