Hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa kan kuɗin rabon tallafi

0
176

Hayaniya ta kaure a zauren Majalisar Dattijai yayin da sanatoci ke muhawara kan zargin cushe a cikin kasafin kuɗin ƙasar, wanda shugaban ƙungiyar sanatocin arewa, Abdul Ningi ya yi a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC.

Tun da farko shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Sen. Olamilekan Adeola daga jihar Ogun ya gabatar da ƙorafi kan tattaunawar da Sanata Ningi ya yi da sashen Hausa na BBC.

Ya soki lamirin kalaman Sanata Ningi kan cewa ana amfani da kasafin kuɗi iri biyu a ƙasar.

Sanata Adeola ya ce wannan tamkar cin zarafi ne da kuma ƙazafi.

KU KUMA KARANTA: Majalisun Dokokin Najeriya sun amince da naira tiriliyan 28.77 a matsayin kasafin kuɗin 2024

Ya bayyana cewa kalaman sanata Ningi ba gaskiya ba ne, kasancewar tun asali babu kuɗin da aka ware a wasu ma’aikatu a cikin kasafin kuɗin da majalisar ta amince da shi.

Sai dai Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi ya bukaci shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya yi adalci wajen jin tabakin Sanata Ningi kan kalamansa a hirarsa da BBC Hausa.

A lokacin da ya yi sa’ilin muhawarar, Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa an yi wa kalaman nasa mummunar fassara ce.

Leave a Reply