Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya za su kafa rundunar tsaron haɗin gwiwa
Gwamnonin shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun amince da kafa tsaron hadin gwiwa da nufin dakile matsalar rashin tsaro a yankin.
Hakan na cikin shawarwarin da kungiyar gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya ta cimma a taron da ta gudanar a Legas a jiya Alhamis.
“Sakamakon karuwar barazanar tsaro, mun yanke shawarar kafa rundunar tsaron hadin gwiwa domin inganta matakan tsaro a fadin yankin kudu maso yamma,” kamar yadda gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya wallafa a shafinsa na X bayan kammala taron na yini daya.
Gwamnan na jihar Legas wanda shi ne shugaban kungiyar ya nanata aniyar gwamnonin ta daukar kwararan matakai domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a tsakanin al’ummominsu”.