Gwamnatin tarayya na shirin biyan ƴan N-Power kuɗaɗensu 

0
420
Gwamnatin Tarayya na shirin biyan ƴan N-Power kuɗaɗensu 
Shugaban ƙasa Tinubu

Gwamnatin tarayya na shirin biyan ƴan N-Power kuɗaɗensu

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na biyan bashin N8bn na alawus-alawus ɗin ma’aikatan shirin N-Power na shekarar 2022 da 2023 bayan ƙarar da suka shigar gaban kotun bisa rashin biyan su wasu haƙƙoƙinsu.

Wannan na zuwa ne yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya jagoranci wani zaman sulhu da wakilai da lauyoyin ’yan N-Power, da kuma gwamnatin tarayya.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya dakatar da shirin N-Power da wasu shirye-shiryen rage raɗaɗin talauci

A yayin zaman sulhun, an cimma yarjejeniya kan biyan alawus-alawus ɗin nan ba da daɗewa ba, wanda hakan ya sa lauyoyin da suka shigar da ƙarar janyewa da ƙarar.

Leave a Reply