Gwamnatin Sudan ta Kudu ta kori shugabannin soji da wasu manyan jami’an ƙasar
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya kori hafsan hafsoshin Ƙasar, da kuma shugaban ‘yan sanda da na gwamnan Babban Bankin ƙasar, kamar yadda wata sanarwa da kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar SSBC ta bayyana.
Sanarwar Kiir ta maraicen ranar Litinin dai ba ta bayyana dalilan korar ba, sai dai ta ce shugaba Kiir ya naɗa Paul Nang Majok a matsayin babban hafsan hafososhin sojojin ƙasar, wanda ya maye gurbin Janar Santino Wol.
Majiyoyin tsaro da ke masaniya kan abubuwan da ke faruwa a cikin rundunar sojin ƙasar, sun bayyana cewa an samu sauye-sauyen ne sakamakon takun-saka tsakanin jami’an rundunar, inda rahotanni ke nuni da cewa wasu sojoji sun shafe kusan shekara guda ba a biya su albashi ba.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Lul Ruai Koang bai mayar da martani nan take ba a lokacin da aka tuntuɓe shi domin jin ta bakinsa.
Michael Makuei, ministan yada labarai kuma mai magana da yawun gwamnati, shi ma bai bayar da amsa kai tsaye ba lokacin da aka nemi da ya yi tsokaci kan dalilan sauye-sauyen.
KU KUMA KARANTA: Burkina Faso ta kori wasu sojoji 14 daga aiki
A ƙarshen watan Nuwamba, yunkurin kama tsohon shugaban hukumar leken asirin ƙasar ya haifar musayar wuta a Juba babban birnin ƙasar.
A farkon watan Oktoba, Kiir ya ƙori Akol Koor Kuc, wanda ya jagoranci hukumar tsaron ƙasar tun bayan da ta samu ‘yancn kai daga Sudan a shekarar 2011, tare da nada wani na kusa da shi domin maye gurbinsa.
A wani sauyi na baya-bayan nan, Kiir ya mayar da Johnny Ohisa Damian a matsayin gwamnan babban bankin ƙasar, inda ya maye gurbin James Alic Garang, wanda ya nada bayan korar Damian a watan Oktoban 2023.
Ya kuma nada Abraham Peter Manyuat a matsayin sabon Sufeto Janar na ‘yan sanda, wanda ya maye gurbin Atem Marol Biar.
A yi ta samun canje-canjen ba zato ba tsammani a fannin shugabancin kasar, musamman ma a ma’aikatar kudi da babban bankin kasa, a ‘yan shekarun nan, inda a shekarar 2020 kadai an maye gurbin gwamnan babban bankin ƙasar sau biyu.
Tattalin arzikin Sudan ta Kuɗu dai ya shiga cikin mawuyacin hali tun bayan yakin basasar da ya barke a shekara ta 2013, wanda ya tilastawa kusan kashi ɗaya bisa huɗu na al’ummarta yin hijira zuwa kasashe makwabta.
Sudan ta kuɗu dai ta samu zaman lafiya tun bayan da aka kawo karshen yarjejeniyar 2018 kan rikicin shekaru biyar da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, amma ana yawan samun tashin hankali tsakanin al’ummomin da ke gaba da juna.
An ɗage lokacin zaɓen ƙasa da aka daɗe ana jira zuwa watan Disamba na shekarar 2026, lamarin da ke nuna ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a tsarin samar da zaman lafiyar ƙasar mai rauni .