Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.
GWAMNAN Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa amincewa ta maido da makudan kudi kimanin Naira biliyan sha takwas (N18b) da Gwamnatin Jihar ta kashe wajen sake gina titunan Gwamnatin Tarayya guda biyar da ke Jihar.
Gwamna Buni ya yi wannan yabon ne a ranar Larabar da ta gabata bayan amincewar da majalisar zartarwa ta tarayya ta yi na mayar wa gwamnatin Jihar kudaden.
Ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin za ta yi amfani da kudaden cikin adalci wajen samar da karin ababen more rayuwa ga yawancin al’umma a fadin Jihar.
A cewarsa, mayar da kudaden zai baiwa gwamnatin Jihar damar gudanar da wasu ayyuka da suka shafi jama’a da za su inganta rayuwar al’umma.”
“Ina so in yaba wa shugaban kasa musamman da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya bisa yadda suke nuna adalci ga Jihar.”
“Alalhakika, samun wadannan makudan kudaden zai ba da gudummawa ga sauran ayyukan da za su yi tasiri ga rayuwar mutanenmu.”
“Gwamnati za ta karkatar da albarkatun zuwa ilimi, samar da kiwon lafiya, samar da ruwan sha, samar da ayyukan yi da sauran ababen more rayuwa domin inganta rayuwar al’ummar mu” Gwamna Buni ya tabbatar.”
Ya bayyana cewa irin wannan fahimtar da ke tsakanin gwamnatocin Jihohi da na tarayya za ta sa gwamnatin Jihar za ta kara kaimi wajen aiwatar da ayyukan Gwamnatin Tarayya da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.
Majalisar zartaswa ta tarayya a zamanta karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta amince wa gwamnatin Jihar Yobe Naira biliyan 18 dangane sake gina wasu hanyoyin Gwamnatin Tarayya guda biyar da Gwamnatin Jihar ta sake ginawa tun tunin.