Gobarar tankar mai ta kashe mutane 20 a Delta

0
165

Aƙalla mutane 20 ne suka mutu sakamakon haɗarin gobarar tankokin man fetur da ya auku safiyar wannan Lahadin a Jihar Delta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kwanar Kokon daura da Gadar Ologbo da ke kan babbar hanyar Warri zuwa Benin a Ƙaramar Hukumar Warri ta Arewa.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra reshen Jihar Delta, Udeme Bassey Eshiet ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai a cewarsa, haɗarin ya rutsa da mutum 15, takwas daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya yayin da bakwai suka samu raunuka.

Kwamandan ya ce waɗanda ƙarar kwana ta cim musu sun ƙone ƙurmus sakamakon haɗarin da ya auku tsakanin motoci 15 ciki har da tankokin mai takwas.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta kashe mutane 11 a gidan rawa a Sifaniya

Ya alaƙanta aukuwar haɗarin da fashewar wata tankar mai ɗaya wanda ya ce tuni jami’ansu da takwarorinsu na hukumar ’yan sanda sun rufe hanyar.

Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa, aƙalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar haɗarin

Wani ganau da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce daga cikin waɗanda ajalin ya katsewa hanzari har da wata mai juna biyu, ƙananan yara da kuma wasu dattawa.

Ya ce bayan faɗuwar tankar ce man da ta ɗauko dakonsa ya riƙa kwarara a kan hanya, lamarin da ya sanya wasu suka riƙa rige-rigen ɗiban rabonsu duk da gargaɗin da direban motar da jami’an tsaro suka yi.

“Mun yi ƙoƙarin hana su, amma wasu matasa suka yi mana barazanar lakaɗa mana duka da cewar ai unguwarsu ce.

“Sun ɗebo mazubi iri-iri suna ɗibar man amma muna samun labarin tashin gobarar da misalin ƙarfe 12:15 na dare muka tsere.

“A yanzu dai ga gawarwaki nan kwance, an tsinto gawarwakin wasu da suka tsere cikin daji suna ci da wuta don ko a yanzu na ƙirga gawarwakin fiye da 20,” a cewarsa.

Leave a Reply