Gobara ta ɓarke a kotun ƙoli a Abuja

0
334

A halin yanzu an samu tashin gobara a kotun ƙoli da ke babban birnin tarayya Abuja.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto ba a san musabbabin tashin gobarar ba, sai dai wata majiya daga hukumar kashe gobara ta tarayya ta ce jami’an kashe gobara na nan a wajen.

An ce an ƙona ofisoshin alƙalai uku. A cewar kafar yaɗa labarai ta ARISE, gobarar ta tilastawa wasu mutanen da ke cikin ginin yin tururuwa domin tsira da rayukansu.

KU KUMA KARANTA: Sakamakon Gobara: Hukumar wutar lantarki a Kebbi, ta yi asarar taransifoma na dala miliyan huɗu

Lamarin gobarar dai ita ce ta baya-bayan nan da ta shafi ofisoshin gwamnati a Abuja.

A watan Mayun 2023, gobara ta ƙone wasu sassan sansanin sojojin saman Najeriya dake kan titin filin jirgin sama a babban birnin tarayya Abuja.

A watan Fabrairun 2022, an samu gobara a ginin ma’aikatar kuɗi da ke Abuja.

A watan Mayun 2020, gobara ta ƙone wani ɓangare na ginin hukumar gidan waya ta Najeriya (NIPOST) a babban birnin tarayya Abuja. Wata guda gabanin faruwar lamarin, gobara ta ƙone wani gini dake ɗauke da ofishin akanta janar na tarayya.

A shekarar 2018, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) ta ce Najeriya ta yi asarar kimanin Naira Tiriliyan 5 sakamakon gobarar da ta faru cikin shekaru huɗu.

Leave a Reply